India: 'Ɓeraye sun shanye dubban litoci na giya'

Berayen Indiya Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sandan gabashin Indiya a jihar Bihar sun ce, beraye sun shanye dubban litocin barasar da aka kwace.

A shekarar da ta gabata ne, kasar ta haramta sayarwa da kuma shan barasar. Tun daga wannan lokacin ne 'yan sandan suka kwace sama da litoci 900,000 na barasa.

Babban jami'in 'yan sanda na birnin Patna, Manu Maharaj, ya ce a ranar Talata ne manyan jami'an 'yan sanda suka shaida masa cewa beraye sun shanye mafi yawan barasar.

Yanzu haka, an bukaci 'yan sandan da su gudanar da bincike a kan hakan.

Babban ministan birnin Bihar, Nitish Kumar ne ya ba da sanarwar haramcin sayar da giyar, ba dadewa ba da kama aikinsa a shekarar da ta gabata.

Giya ta kashe leburori 17 a Indiya

Ana ganin haramta shan giyar hanya ce ta rage cin zarafin mata a gidajen aure da kuma talauci.

Bayan daukar matakin ne sai jami'an 'yan sandan sun kaddamar da aikin bincike a jihar don kwace barasar. Sun kuma kama sama da mutum 40,000, wadanda ake zargi da ajiye barasar a gidajensu da kuma shaguna, wanda hakan ya sabawa ka'ida.

Sakamakon binciken da 'yan sanda suka yi ya sa aka kama kwalaben barasa masu yawan gaske, wadanda aka ajiyesu a caji ofis a matsayin sheda.

Wasu caji ofis din ma sai da suka yi hayar wuraren da za su ajiye kwalaben barasar.

Hakkin mallakar hoto Prashant Ravi
Image caption 'Yan sanda sun kwace dubban litoti na barasar da suka kwace a bara sakamakon hana shanta da aka yi

Yanzu haka, sama da caji ofis 1,000 ne a kasar aka umarta da su gudanar da bincike a wuraren da aka ajiye barasar da aka kwace.

Mista Maharaj, ya shaidawa jaridar Hindu cewa, har ila yau jami'an za su ci gaba da gudanar da bincike a kan sha da sayar da barasar.

Ya ce, "Baya ga gurfanar da su da za a yi a karkashin sabuwar dokar biyan haraji da kuma dokokin da aka haramta, idan aka same su da laifi a binciken da za a yi, za su iya rasa aikinsu".

A dokar kasar, idan aka samu wani da sha ko sayar da barasa, za a daure shi tsawon shekara goma a gidan yari.

Labarai masu alaka