Hotunan Shugaba Buhari a masallacin Juma'a

Haruna Tangaza ya dauko mana wasu hotunan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a lokacin da ya fito sallar Juma'a.

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ya fita masallacin ne da ke cikin fadarsa da misalin karfe 1.30 na rana, ya kuma zauna ya saurari huduba kafin daga bisani aka tayar da sallah.

Bayanan hoto,

Shugaban ya je masallacin ne a karkashin rakiyar manyan mukarransa da masu tsaron lafiyars, inda ya shafe minti 12 a cikin masallacin.

Bayanan hoto,

Haruna Tangaza ya ce akwai alamun lafiyar shugaban ta inganta a ganin da ya yi masa a yau fiye da mako biyu da ya gabata lokacin da ya fito sallar Juma'a.

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya gaisa da mutane da dama da suka hada da mai ba shi shawara a kan harkar tsaro Babagana Munguno da shugaban ma'aikatansa Abba Kyari da wasu da dama, bayan kammala sallar.

Bayanan hoto,

Haruna ya ce da wuya ka gane wata alama ta rashin lafiya a tare da shi ta salon tafiyarsa da maganarsa, baya ga 'yar ramar da ya yi kawai.

Bayanan hoto,

"Shugaba Buharin ya yi 'yar raha kamar yadda ya saba a yayin da yake gaisawa da mutane, ya kuma ta dagawa wadanda ke nesa da shi hannu alamun gaisuwa," In ji Haruna.