Jirgin da China ta kera ya tashi da fasinjoji a karon farko

Jirgin China Hakkin mallakar hoto AFP

A karon farko kasar China ta kera wani katafaren jirgin fasinja wanda tuni tayi nasarar kammala gwajinsa, lamarin da zai kawo kalubale ga kamfanonin Boeing da Airbus.

Bayan kimanin mintuna 90 yana shawage a sararin samaniya, jirgin ya sauka babu matsala a filin saukan jiragen sama na Pudong dake Shanghai.

Kera wannan jirgin yana nuna alamar burin da kasar Sin ke da shi na shiga harkar kirar jiragen fasinja.

Kamfanin Comac wanda mallakin gwamnatin kasar Sin ne ya kera wannan jirgin, kuma tun shekara ta 2008 kasar ta Sin ke shirin wanda bai sami kammaluwa ba sai yanzu.

Jirgin ya tashi da matuka da injiniyoyin jirgin guda biyar ne kawai, a ranar Jumma'a, inda dubban jama'a da suka hada da manyan jami'ai da ma'aikata da kuma masu sha'awa suka hallara ganin tashin jirgin.

Kamin tashin jirgin, tashar talabijin mallakin gwamnatin Sin ta bayyana cewa jirgin zai yi tafiya da bata wuce tsawon mita dubu 3 ba (kafa 9,800), wanda bai kai tsawon da aka saba yi ba idan da jirgin yana dauke da fasinja ne, da misalin mita dubu 7, kuma zai yi gudun kilomita 300 ne a kowace sa'a (mil 186).

An tsara wannan jirgin mai sunan C919 don yayi gasa kai tsaye da jiragen Boeing 737 da na Airbus A320.

A wata hira da aka yi da Cai Jun wanda shi ne matukin jirgin a watan Maris, amma aka nuna hirar a tashar talabijin na kasar Sin dab da gwajin tashin jirgin, yace yana cike da karfin gwuiwa game da ingancin jirgin.

"Matukin jirgi ya san halin da jirgi yake ciki. Ya na iya sanin idan jirgin zai iya tashi. Saboda haka bana fargabar komai, sai dai na mayar da hankali ne kan ingancin jirgin a yanzu" inji shi.

Ya bayyana yadda ya dakatar da wani gwaji a shekarar 2016 saboda wata matsala da birkin jirgin.

Yace "Abin kamar tukin mota ne. Da na taka birkin jirgin kawai sai ya fara girgiza".

Yace gardamar da rika yi da injiniyoyin jirgin ya taimaka wajen tabbatar da ingancinsa.

"Ga injiniyoyin, wannan jirgin tamkar da ne a garesu, wanda suke ganin bashi da wani laifi. Amma aikin mu shi ne mu tabbatar masu cewa wannan dan nasu yana da laifuka, yana da inganci kuma yana da rauni, kuma dole su kara kaimin inganta shi."

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jirgin alfahari na kasar Sin

•Jirgin samfurin C919 yana da injina biyu, kuma yana iya daukar fasinjoji 168.

•Zai iya tafiya mai nisa daga kilomita 4,075 zuwa kilomita 5,555 (mil 2,532 - mil 3,452).

•Kafofin watsa labaran kasar Sin sun yi hasashen tsadar jirgin zai kai dalar Amurka miliyan 50, wanda yake kasa da rabin farashin jiragen Boeing 737 da na Airbus A320.

Amma yawa-yawan bangarorin jirgin ana shigo dasu daga kasashen waje ne. A misali kamfanin CFM mallakin kasar Faransa da Amurka ne ya kera injinan jirgin.

Jami'ai sun ce tuni aka sami odar sayen jirage fiye da 500, daga wasu kamfanoni 23 na kasar ta Sin. Babbar odar ta fito ne daga kamfanin China Eastern Airlines.

Hukumar kiyaye hadura ta nahiyar Turai ta fara duba cancantar bada lasisi ga jirgin na C919 - wanda shi ne muhimmin mataki na samin shiga kasuwannin duniya.

Kasar Sin ta dade tana son kera jirgin fasinja tun shekarun 1970, a lokacin da uwargidan tsohon shugaban kasar Mao Zedong mai suna Jiang Qing ta mara ma wani yunkurin yin haka.

Amma wannan jirgin a kera mai suna Y-10 bai yi nasara ba domin yawan nauyin sa. Kana guda uku kawai aka kera.

An kiyasta nan da shekaru 20 masu zuwa, kasuwar kere-keren jiragen sama zai zarce dalar Amurka tiriliyan 2 (Fam tiriliyan 1.55).

Labarai masu alaka