'Bai wa aladu ruwa ba zai sa a ɗaure mutum ba'

Anita Krajnc
Bayanan hoto,

Masu fafutuka sun wallafa bidiyon yadda lamarin ya wakana a intanet

Wani alkali da ke birnin Ontario ya yi watsi da tuhumar da ake yi wa Anita Krajnc mara tushe wanda ya kawo karshen tashin hankalin da ya ja hankulan masu fafutukar 'yancin dabbobi.

Alkali David Harris ya ce bai gamsu cewa Mis Krajnc ta kyeta dokar amfani da waje ba a lokacin da ta shayar da aladun ruwa daidai lokacin da za a kai su mayanka.

Mis Krajnc ta ce ta tabbatar da cewa, "tausayi ba laifi ba ne".

Yin abin da bai dace ba a filli ko gidan wani laifi ne a Canada.

Alkali Harris ya rubuta a hukunci da ya yanke cewa ya gamsu Ms Krajnc "bata yi shishigi ko kutse a wuri ko gidan wani ba tare da izini ba a cikin watan Yulin shekarar 2015, a lokacin da ta bai wasu aladu 190 da aka yi dakonsu a wata motar a-kori-kura zuwa mayanka a wajen birnin Toronto.

Ms Krajnc wacce tare da wasu suka samar da wata kungiyar kare Aladu ta Toronto Pig Save a shekarar 2011, su kan gana da wasu masu fafutuka a kan wani tsibiri da ke kusa da mayankar domin hilatarsu kuma su basu ruwa.

Amma a wannan karon sai matukin a-kori-kurar ya tunkari Mis Krajnc kuma aka kira 'yan sanda.

Masu fafutuka sun wallafa bidiyon yadda lamarin ya wakana a intanet.

Bayanan hoto,

Kungiyoyin masu fafutukar kare dabbobi sun gudanar da kamfe makamacin haka a wasu sassan duniya

A lokacin da ake sauraron kararta, dakin da ake sauraron karar a kotun ya cika makil da magoya bayanta inda da dama ma suka zauna a kasa.

Duk da nasarar da ta yi a ranar Alhamis, Ms Krajnc ta shaidawa BBC cewa, "bata gama gamsuwa" da hukuncin da aka yanke ba.

"Fatanmu shi ne tsarin mulkin kasar ya dauki aladu da sauran dabbobi ma ba kawai a matsayin kadara ba, ta ce muna so su gane cewa su ma suna da 'yanci.

A hukuncin da alkali Harris ya yanke ya ce a karkashin dokar Canada, alade kadara ce.

Ya kara da cewa, "Mis Krajnc da masu irin ra'ayinta za su iya yarda da hakan ko akasin haka."

Kungiyoyin masu fafutukar kariya sun gudanar da kamfe makamacin haka a wasu sassan duniya har ma da Birtaniya.