Kungiyoyin ba da agaji sun janye daga sassan jamhuriyar CAR

Jamhuriyar tsakiyar Afirka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana shan kai hare-hare kan sansanonin kungiyoyin bayar da agaji a Jamhuriyar Tsakiyar Afirka

Majalisar Ɗinkin ɗuniya ta bayyana damuwa a kan janyewar kungiyoyin ba da agaji daga arewacin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya saboda ƙaruwar hare-haren da ake kai wa jami'ansu.

Ta ce wasu jerin hare-hare kan sansanonin masu ba da agajin jin-ƙai ne suka sa yanayin ya kasance mai matuƙar hatsari ga jami'an agaji su iya gudanar da ayyukansu a arewacin kasar.

Majalisar Ɗinkin Duniyar ta ce an kai hare-hare 16 kan sansanonin kungiyoyin ba da agaji tun daga watan Maris.

Kungiyoyin ƙasashen waje masu ba da agajin jin-kai 14 ne suka janye inda suka daina gudanar da ayyukansu a yankin Ouham, yayin da ƙungiyar likitocin sa-kai ta Doctors Without Borders ta taƙaita aikinta ga ba da taimako kawai ga wadanda ke fama da matsanaciyar jinya.

Jami'in bayar agajin jin-kai na Majalisar Dinkin Duniya a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Michael Yao ya ƙididdige cewa mutane fiye da miliyan 2 ne ke bukatar agajin abinci da magunguna a kullum.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mutane za su dandana kudarsu muddin kungiyoyin agaji suka fice daga Jamhuriyar Tsakiyar Afirka in ji MDD

Kungiyoyin ba da agajin dai sun yi ƙaura zuwa Bangui babban birnin ƙasar, inda nan ne ya fi kwanciyar hankali.

Mr Yao ya ce mutane za su ɗanɗana kuɗarsu muddin ƙungiyoyin ba da agajin suka fice daga ƙasar.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta auka kazamin rikici a shekara ta 2013, lokacin da ƙungiyar 'yan tawayen Seleka wadda galibi 'ya'yanta musulmai ne suka kwace mulkin kasar.

Daga bisani ne kungiyar masu gwagwarrmaya da makamai da akasari su kuma Kiristoci ne suka mayar da mummunan martani.

Tun daga wannan lokaci ne kungiyoyi masu rike da makamai da ba sa ga maciji da juna suka ci gaba da gwabza fada.

Gwamnatin kasar dai na rike da iko da Bangui babban birnin kasar ne kawai.

Labarai masu alaka