'An yi wa dan takarar kasar Faransa kutse'

Zaben kasar Faransa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kawo karshen yakin neman zabe kafin kada kuri'ar ranar Lahadi

Ayarin yaƙin neman zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasar Faransa da ke kan gaba-gaba, Emmanuel Macron ya ce an yi masa gagarumin kutse, bayan fallasa wasu dubban takardu a intanet.

An fallasa takaradun ne a wani shafin yada bayanai na intanet a yammacin Jumma'a, yayinda ake daf da kawo karshen yakin zaben shugaban kasa.

Mashawartan Macron sun ce an gauraya saƙwannin imel da aka sata daga akwatunan ƙusoshin jam'iyyarsa da wasu na jabu don sanya wasu-wasi, da ba da bayanai marasa sahihanci.

Suka ce masu kutsen ƙarara na son yi wa yaƙin neman zaɓensa maƙarƙashiya da kuma wargaza dimokraɗiyya kafin kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen a gobe Lahadi.

An yi wa 'yan takara da kafafan yada labarai iyaka, har sai an gama kada kuri'u ranar Lahadi, a hakan ke nufi Mr Macron ba zai iya fitar da karin wasu sanarwa ba.

Binciken jin ra'ayoyin jama'a sun nuna tsohon ministan tattalin arziki ne kan gaba da maki kashi 20 bisa dari ko fiye da haka kan Ms Le Pen.

Labarai masu alaka