'Yan Venezuela na son Mista Maduro ya yi murabus

Masu bore a Venezuela
Image caption Shugaba Nicolas Maduro na shan suka daga 'yan siyasa da kungiyoyin fararen hula

A harbe har lahira wani matashi a birnin Valencia na kasar Venezuela, a lokacin wata zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Nicolas Maduro.

Wannan dai shi ne kisa na baya-bayan nan da aka yi wa masu zanga-zangar, wasu matasa sun fasa shagunan mutane a wasu biranen kasar tare da yi musu sata.

Rahotanni sun bayyana cewa an tunbuke mutum-mutum tsohon shugaban kasar marigayi Hugo Chabez da aka kafa a jihar Zulia tun bayan mutuwarsa.

Akallah mutane talatin ne suka mutu, wasu daruruwa kuma suka jikkata a zanga-zangar da aka kwashe makwanni ana yi a kasar, inda ma su suka bayyana matakin da shugaba Maduro ke dauka na karawa kan sa madafun iko da abu ne da ba zai taba yiwu wa ba.

Wasu na ganin manufofin gwamnati, da tsare-tsaren farfado da tattalin arzikin kasar ba su wadata ba, inda kayan masarufi da na bukatun yau da kullum sukai matukar tsada.

A gobe lahadi ne kuma aka shirya matan kasar za su yi jerin gwano duk dan kan adawa da shugaban kasar ta Venezuela.

Labarai masu alaka