Iskar gas ta illata ɗalibai a India

Daliban makarantar a lokacin da aka kai su asibiti
Image caption Ministan lafiyar India ya bai wa asibitin Central Gol umarnin kula da daliban a kyauta

Akalla dalibai 200 na wata makaranta da ke birin Delhin India ne aka tabbatar da an kwantar da su a asibiti bayan sun shaki iskar gas sanadiyyar bulewar bututun wurin da ake ajiye shi.

Daliban makarantar Rani Jhansi sun fara korafin idanunsu na kaikayi, sannan makogwaronsu na bushewa, kuma makarantar na kusa da wurin da ake ajiye gas din.

An yi amanna da cewa iskar gas din ya na kunshe da sinadarin chloromethyl pyridine, wanda masana'antu ke amfani da shi, dan hada maganin sauro da kwari.

An dai kwashe daukacin daliban makarantar da ke yankin Tughlakabad, sai dai har yanzu ba a bayyana ko daliban na cikin mawuyacin hali ba.

Shugaban hukumar kashe gobara a jihar Delhi, Atul Garg ya ce tuni aka aike da jami'an kashe gobara da taimakon gaggawa makarantar gwamnati da 'yan mata ne zalla a cikin ta.

Hukumar kare bala'i da jami'an tsaron birnin Delhi, sun tabbatar da babu dalibar da ta shiga mawuyacin hali, ko rasa rai.

A bangare guda kuma ministan lafiyar India ya wallafa a shafin sa na twitter cewa ya na yi wa 'yan uwa da iyayen daliban jaje.

Za kuma a dauki matakin hakan ba ta sake faruwa ba.

Labarai masu alaka