Ismail Haniya ne sabon shugaban Hamas

Ismail Haniya
Bayanan hoto,

Kungiyar Hamas ta dade ta na gudanar da ayyukanta a yankin zirin Gaza

Kungiyar masu tayar da kayar baya ta Hamas, mai mazauni a kasar Labanon, ta sanar da zabar tsohon Firai ministan ta Ismail Haniya a matsayin sabon shugaban kungiyar.

Ya gaji Khaleed Meshaal wanda ya jagoranci kungiyar har sau biyu.

Mista Haniya - mai shekara 42 - yana zaune ne zirin Gaza inda kungiyar Hamas take mulka tun shekarar 2007, ba kamar Mista Meshaal ba da ya yi rayuwarsa a kasar Qatar.

Ana yi wa Haniya kallon jarumi, wanda zai kawo sauyi da sassaucin rikicin da kungiyar Hamas ke yi da kasashen yammacin duniya.

Mai magana da yawun Hamas Fawza Barhoum ya tabbatar da cewa cancanta ce ta sanya aka zabi Mista Haniya.

Kungiyar dai ta wallafawa wasu sabbin dokoki da kudurinta, wanda ake ganin masu sassauci ne da nufin farfado da martabarta a idon duniya.

Wanda kungiyar ke kallon sabbin dokokin za su ba ta damar cudanya da duniya baki daya.

A cikinsa Hamas ta sake nanata ba wai bata amince da 'yancin Isra'ila ba, ko wanzuwarta don haka ba za ta kara tashin hankali da kasar ba matukar ba takalar ta aka yi ba.

Sai dai a nasa bangaren mai magana da yawun Firaiminstan Isra'ila Baenjamin Netanyahu, ya ce babu wani kalami ko mataki da kungiyar Hamas za ta dauka da za ta burge Isra'ila.

Hasali ma kalaman na yaudara ne, kuma ba za su taba nasara a kansu ba.