Tottenham na da damar daukar kofin Premier - Pochettino

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Pochettino ya ce zai yi matukar wahala sun tarar da Chelsea

Kocin Tottenham Mauricio Pochettino ya ce har yanzu kungiyar ba ta karaya ta bar wa Chelsea damar cin kofin Premier ba, sai dai ya amince cewa zai yi matukar wahala su dauki kofin bayan kashin da suka sha a hannun West Ham.

Tottenham na bayan Chelsea da maki hudu bayan kwallon da Manuel Lanzini ya ci wa West Ham ta ba su damar doke Tottenham da ci 1-0 a filin wasa na London Stadium.

Chelsea,wacce za ta karbi bakuncin Middlesbrough ranar Litinin, na bukatar cin wasa biyu a cikin wasa hudun karshe da za su yi kafin ta dauki kofin.

Pochettino ya ce, "Har yanzu bamu karaya ba. Za mu ci gaba da jira amma muna ganin da wahala mu tarar da Chelsea."

"Ba na tayar da hankalina. Kuma ba na takaici tun da dai mun barar da damar da muka samu ta cike gibin da ke tsakaninmu," in ji shi.

Tuntuni Chelsea ta nuna alamar lashe kofin Premier na biyu a cikin kakar wasa uku, saboda ita ce ke ta daya a saman tebirin gasar tun tsakiyar watan Nuwamba.

Nasarar da Tottenham suka yi a wasa tara a jere, da kuma dokewar da Crystal Palace da Manchester United suka yi wa Chelsea, sun sanya wa Tottenham din fatan daukar kofin na Premier, a karon farko tun 1961.

Da a ce sun doke West Haram za su cike gibin da ke tsakaninsu da Chelsea da maki daya, amma hakan ya gagara.

Labarai masu alaka