DSS ta kama fitaccen dan kasuwar Nigeria Ifeanyi Ubah

Ana zargin Mr Ubah da sace man NNPC Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin Mr Ubah da sace man NNPC

Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kama fitaccen dan kasuwar nan na man fetur a Ifeanyi Ubah saboda zarginsa da yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

"A matsayinta na mai yin bincike kan laifukan da suka shafi tattalin arziki da tsaron kasar, DSS ta kama Ifeanyi Ubah, babban daraktan kamfanin man fetur na Capital Oil and Gas Limited ranar biyar ga watan Mayu", in ji wata sanarwa da kakakin hukumar Tony Opuiyo ya aike wa manema labarai.

Sanarwar ta kara da cewa an kama Mr Ubah ne saboda zarginsa da laifukan da suka hada da sata, da karkatarwa da kuma sayar da man fetur din da babban kamfanin mai na kasa, NNPC ya ajiye a tankunansa.

Sai dai har yanzu Mr Ubah bai ce komai a kan wannan zargi ba.

DSS ta ce ta gano cewa man da Mr Ubah ya sace ya kai na N11bn, lamarin da zai yi mummunar illa ga tattalin arzikin kasar.

A kwanakin baya ne NNPC ya kori wasu manyan jami'ansa, cikinsu har da Mrs. Esther Nnamdi-Ogbue, wacce aka samu da sakaci wurin aiki lamarin da ya yi sanadiyar 'batan' man fetur wanda ya tasamma kusa da N11bn.

Bincike ya gano cewa jami'an na NNPC sun ajiye man ne a ma'ajiyar man kamfanin Mr Ifeanyi Ubah, shi kuma ya sayar da shi ba tare da saninsu ba.

Labarai masu alaka