Ko za a iya ceto 'yan matan Chibok kuwa?

Chibok
Image caption Wasu daga cikin 'yan matan da aka gano sun dawo da yara

A ranar Juma'a ne aka cika shekara uku daidai da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace wasu 'yan mata fiye da 200 da ke rubuta jarrabawa a makarantar sakandaren garin Chibok da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

Al'amarin ya ja hankalin duniya kwarai. Wanda hakan ya sa aka fara fafutikar ganin an ceto su.

Tun a lokacin mulkin tsohon shugaban kasar Goodluck Jonathan da aka sace yaran, kasashen duniya da dama kamar Amurka da Birtaniya da Faransa da China sun yi alkawarin taimakawa Najeriya wajen ganin an ceto 'yan matan, sai dai har ya sauka daga mulki ba a ji ko da duriyarsu ba.

Jakadakan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright, a lokacin da ya kawo ziyara ofishin BBC da ke Abuja ranar Talata, ya ce tun bayan sace 'yan matan ne kasarsa da kuma sauran kasashen duniya suka fara bai wa Najeriya taimako ta fuskar bai wa dakarun kasar horo da kuma bayanan sirri.

Sai dai duk da wannan ikirari nasa na baya-bayan nan da ke nuna cewa sun dade suna aiki don gano maboyar yaran, an kwashe lokaci mai tsawo kafin haka ta fara cimma ruwa, inda aka gano yarinya ta farko mai suna, Amina Ali Nkike, a cikin watan Mayun 2016.

'Yan kwanaki bayan haka ne kuma yarinya ta biyu ta kara bayyana.

Sai dai daga nan ba a kara jin duriyar sauran yaran ba har sai a cikin watan Oktobar 2016 din, inda aka sako wasu guda 21 daga cikinsu, bayan wata yarjejeniya da aka cimma da kungiyar Boko Haram.

Hakazalika, a watan Janairun 2017 ma, rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake gano wata yarinya daga cikin 'yan matan.

A duk lokacin da aka samu labarin ceto wasu daga cikin 'yan matan a kan yi maraba da hakan, daga iyayensu har zuwa mahukunta da kuma al'ummar kasa.

Image caption Boko Haram ta taba cewa ta musuluntar da 'yan matan wadanda mafi yawansu Kiristoci ne

Sai dai a kan so a ji halin da sauran suke ciki da kuma lokacin da za a kai ga 'yanto su duka.

Ganin lokaci da aka kwashe ana dakon ganin an ceto su gaba daya, ya sa wasu suke ganin an ya kuwa za a iya samo sauran da suka rage? Musamman idan aka yi la'akari da yadda matsin lambar da mahukunta suke fuskanta don ganin an ceto yaran yana ci gaba da raguwa.

Hakan yana ci gaba da fitowa fili ne tun bayan da aka yi nasarar ceto wasu daga ciki.

'Da ma mun fada Jonathan bai so ceto 'yan Chibok ba'

Bai kamata duniya ta manta da mu ba - 'Yar Chibok

An yi ta cacar-baka tsakanin gwamnati da 'yan kungiyar da ke fafutikar ganin an ceto 'yan matan Chibok din, wato BBOG, inda take zargin gwamnati da gazawa wajen shiga dajin Sambisa wurin da ake zargin nan Boko Haram ta boye 'yan matan.

Hakan ya sa dakarun Najeriya suka kai jagoran BBOG Oby Ezekwesili da Aishetu Yusufu da wasu mukarrabansu zuwa dajin Sambisan don ganewa idonsu kokarin da hukumomi suke yi don nemo sauran 'yan matan.

Sai dai wasu na ganin cewa da wuya mahukunta a kasar su iya wa wanke kansu gaba daya daga laifi, musamman ma yadda wasu suke ganin akwai sakaci tun farko game da yadda gwamnatin jihar Barno ta bari daliban suke je makarantar don zana jarrabawa, ganin yadda ake fuskantar barazanar tsaro a lokacin.

Akwai kuma wasu da suke ganin bai kamata a tattara hankali kawai a kan 'yan matan Chibok ba. Hasali ma ba su kawai Boko Haram ta taba sace wa ba, don a Damasak ma, wani gari a jihar Bornon, an sace daruruwan mata da yara.

Har ila yau, akwai kuma masu ganin ya dace a rika tunawa da batun daliban da aka kashe a kwalejin gwamnatin tarayya da ke garin Buni-Yadi da kwalejin koyon aikin gona ta Gujuba duka a Jihar Yobe.

Image caption An gano wasu daga cikin 'yan matan lokacin mulkin shugaba Buhari

Alkawarin kasashen waje

Jakadakan Birtaniya a Najeriya Paul Arkwright ya bayar da tabbacin cewa Birtaniya za ta ci gaba da bayar da taimakonta don ganin haka ta cimma ruwa.

Har ila yau, ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin kasarsa da kuma Najeriya ta fuskar yaki da ta'addanci. Kuma kasarsa ta yi aiki tare da Najeriya kama daga gwmnatin Goodluck Jonathan zuwa ta Muhammadu Buhari don ganin an ceto 'yan matan.

Amma Mista Arkwright ya ce ba gaskiya ba ne zargin da masu fafutikar ganin ceto 'yan matan suke yi cewa karsashin dakarun Najeriya da kuma kasashen duniya ya ragu wajen ganin an ceto 'yan matan.

"Na taba ganawa da iyayen yaran da kuma wasu mambobin kungiyar BBOG, amma ba su taba yi mini korafi ba game da cewa Birtaniya ba ta ba da goyon bayan da ya dace ba," in ji Mista Arkwright.

Ya ce idan akwai wani zargin gazawa daga bangaren gwamnatin Najeriya, ita ce ta fi dacewa ta mayar da martani kan hakan, ba kasarsa ba.

Sai dai jakadan Birtaniya ya ce ba abu ba ne mai sauki a ceto 'yan matan gaba daya ba.

"Saboda bayan sace su an warwatsa su ne wurare daban-daban, amma ba mu manta da su ba. Kuma a wannan lokaci da ake cika shekara uku da sace su kamata ya yi mu kara rubanya kokarinmu.

Za mu ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Najeriya da sauran kasashe don mu tabbatar da cewa an ceto su."

Me ya sa aka shafe tsawon lokaci ba duriyarsu?

Image caption Mista Arkwright ya ce Birtaniya za ta ci gaba da taimakon Najeriya don ceto sauran 'yan matan

An tambaye Mista Arkwright kan ko me ya sa aka dauki lokaci mai tsawo ba tare da ceto su ba ganin yadda ake tattara bayanan sirri da kuma kwararrun da ake da su?

Sai ya ce, "Ba zai yiwu a ce mun nuna wurin da ake boye da su ba."

"Sai dai za mu iya ba da taimako da dakaru, kuma yana da kyau a fahimci cewa ba za mu iya shiga dajin Sambisa ba don kubutar da 'yan matan da kanmu. Wannan wani abu ne da ya dace dakarun Najeriya su yi. Kuma za mu tallafa musu," in ji shi.

Ko Birtaniya za ta iya tura dakaru na musamman don ceto su?

"Wannan babbar magana ce. Don gwamnati ba ta nemi hakan ba. A baya Najeriya ta kan bukaci tallafi ne da ya shafi horar da dakaru da musayar bayanan sirri da sauransu, amma ba ta nemi mu tura dakaru na musamman ba," a cewar Mista Arkwright.

A yanzu dai a iya cewa, duniya za ta zura ido ne don ganin ko gwamnatin Najeriya da sauran kasashen duniya da suka yi alkawarin taimakawa za su cika wannan alkawari nasu ko a'a.

Labarai masu alaka