Bama-baman Yaƙin Duniya na 2 sun tilasta kwashe Jamusawa

Kasar Jamus Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An jefa bama-baman ne lokacin Yakin Duniya na Biyu amma ba su tashi ba

Mahukuntan Hanover a arewacin ƙasar Jamus na kwashe mutum dubu 50, kashi 10 cikin 100 na al'ummar birnin, don kawar da wasu bama-baman da aka jefa a lokacin Yaƙin Duniya na Biyu amma ba su tashi ba.

Mutanen za su bar gidajensu da ƙarfe takwas na safe a ranar Lahadi, don bai wa ƙwararrun masu kwance bam damar ɗauke aƙalla irin wannan bam guda biyar a wani waje da ake ginawa.

Ana iya shafe tsawon ranar ko ma fiye da haka ana aikin, matuƙar aka gano ƙarin wasu bama-bamai.

Jiragen yaƙin dakarun ƙawance a lokacin Yaƙin Duniya sun kai wa Hanover hari sau 125 don karya lagon Jamusawa.

Sama da kashi 20 cikin 100 na bama-baman da suka jefa a lokacin sun gaza tashi.

Labarai masu alaka