'Musaya muka yi da BH don kuɓutar da 'yan Chibok'

'Yan matan sakandaren Chibok
Image caption Wasu daga cikin 'yan matan sun yi nasarar tserewa tun lokacin da Boko Haram ta sace su

Gwamnatin Nijeriya ta ce ta yi musayar mayaƙan Boko Haram da ƙungiyarsu don kuɓutar da 'yan matan sakandaren Chibok 82.

A baya ma,, ƙungiyar 'yan tada-ƙayar-bayan ta saki 'yan matan Chibok guda 21.

Sama da shekara uku kenan da sace 'yan makarantar sakandaren kusan 300 a garin Chibok na jihar Borno a arewa maso gabashin Nijeriya.

Mataimakin na musammam kan harkokin yaɗa labarai ga shugaban Nijeriya, Mallam Garba Shehu ya ce a ranar Lahadi ne shugaba Muhammadu Buhari zai karɓi 'yan matan da aka sako.

Image caption Iyayen 'yan matan Chibok sun sha bayyana cewa ba su fitar da rai a kan sake ganawa da 'ya'yansu da aka sace ba

"An yi wata da watanni ana tattaunawa....da gudunmawar ƙungiyoyi daban-daban... da kuma ita kanta ƙasar Switzerland.

Wannan tattaunawa da aka yi, sai aka cim ma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Nijeriya da su 'yan ƙUngiyar, wanda gwamnati ta karɓi 'yan mata...

Su kuma aka ba su wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyarsu da ke hannun gwamnatin Nijeriya a yanzu, in ji Garba Shehu"

Ya ce ana sa ran samun cikakken jawabi game da ko 'yan Boko Haram nawa gwamnati ta bayar a madadin 'yan matan Chibok 81 daga bakin shugaban ƙasar kansa.

Da aka tambaye shi, anya gwamnati ba ta yi raguwar dabara, sakin 'yan Boko Haram da ka iya ci gaba da kai hare-haren da za su yi sanadin mutuwar rayukan 'yan Nijeriya?

Garba Shehu ya ce "Ai mu ba ma fatan haka, cewa wannan abu zai je ya kawo wata ɓarna a nan gaba."

A cewarsa irin wannan tattaunawa idan aka fara ai ba a san yadda za ta kaya ba.

Tana iya yiwuwa wannan ya zama mataki na gina ƙarin wasu yarjejeniyoyi nan gaba wataƙila sulhun da ake nema ya zama na dindindin, in ji Garba Shehu.

Labarai masu alaka