Uwar bama-bamai ba ta da wata rana - Fafaroma

Pope Francis Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fafaroma ya fusata da sanya wa bam sunan uwa

Fafaroma Francis ya soki lamirin sanya wa ƙaton bam ɗin da sojan Amurka suka taɓa amfani da shi a wajen yaƙi sunan "uwar bama-bamai".

Fafaroma ya faɗa wa wani taron ɗalibai a fadar Vatican cewa "Sai kunya ta kama ni da na ji wannan suna."

"Ai uwa silar rayuwa ce, wannan kuma silar mutuwa yake, kuma mu kira wannan abu uwa. Me yake damunmu?" ya tambaya.

A cikin watan jiya ne, Amurka ta jefa irin wannan bam, mai nauyin kilogram 9,800 kan 'yan tada-ƙayar-bayan IS a ƙasar Afghanistan.

Ma'aikatar Pentagon ta ce wani jirgin Amurka ya jefa bam ɗin a lardin Nangarhar, a kan wani kogo da mayaƙan IS ke amfani da shi.

A hukumance ana kiran bam ɗin da suna GBU-43/B Massive Ordnance Air Blast Bomb (MOAB), ko da yake sunan "uwar bama-bamai" ya fi fitowa fili.

A shekara ta 2003 aka fara gwada shi, amma ba ta taɓa amfani da shi a yaƙi ba kafin na Afghanistan.

Kalaman Fafaroma sun zo ne gabanin tattaunawar da zai yi da shugaban Amurka Donald Trump a ranar 24 ga watan Mayu.

Labarai masu alaka