Musayar matan Chibok: Anya ba za a bar baya da ƙura ba?

Kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da mutum 20,000 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kungiyar Boko Haram ta kashe fiye da mutum 20,000

Musayar da gwamnatin Najeriya ta yi, inda Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok 82, yayin da ita kuma ta mika wa kungiyar wasu dakarunta da ake tsare da su, ta aza ayar tambaya: anya ba za a bar baya da kura ba?

'Yan matan na cikin mata 276 da Boko Haram ta sace a watan Afrilun 2014, lamarin da ya jawo wa gwamnatin wancan lokacin kakkausar suka daga duk fadin duniya.

Mai magana da yawun Shugaba Muhammadu Buhari, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa: "An yi wata da watanni ana tattaunawa tsakanin gwamnati da shugabannin Boko Haram tare da gudunmawar ƙungiyoyi daban-daban da kuma ƙasar Switzerland.

"Wannan tattaunawa da aka yi, sai aka cim ma yarjejeniya tsakanin gwamnatin Nijeriya da su 'yan ƙungiyar, wanda gwamnati ta karɓi 'yan mata su kuma aka ba su wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyarsu da ke hannun gwamnatin Nijeriya a yanzu."

Sai dai bai fadi adadin 'yan Boko Haram din da gwamnati ta saka ba.

Amma wasu na nuna dari-dari ga wannan musaya da gwamnatin Najeriya ta yi, inda suke ganin cewa kamar an kashe miciji ne ba tare da sare kansa ba.

Suna ganin sakin dakarun Boko Haram din wata gurguwar dabara ce, wacce za ta iya karfafa gwiwar 'yan kungiyar su ci gaba da hare-haren da suke kai wa.

Wasu mazauna jihar Borno sun nuna rashin gamsuwa da yadda aka aiwatar da wannan musayar.

Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption An kai 'yan matan asibiti kafin su tafi fadar shugaban kasa
Hakkin mallakar hoto NIGERIAN GOVERNMENT
Image caption Akwai alamar gajiya a jikinsu

"Muna farin ciki da yadda aka sako 'yan matan Chibok, amma babu shakka ina da damuwa kan yadda aka ce an saki mayakan Boko Haram," a cewar wani jami'in gwamnatin Borno wanda ya nemi a boye sunansa.

Ya kara da cewa "me hakan ke nufi, ina za mu sa kanmu? Wannan ba karamin koma-baya ba ne a ganina".

Sai dai fadar shugaban kasar ta ce ba haka abin yake ba.

A cewar Malam Garba Shehu, "Ai mu ba ma fatan haka, cewa wannan abu zai je ya kawo wata ɓarna a nan gaba."

Shi ma Malam Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Consultancy da ke nazari kan sha'anin tsaro a Afirka, ya shaida min cewa musayar 'yan matan ba za ta kawo wata barazana ba, musamman ganin cewa ba wannan ne karon farko da aka yi haka ba.

Ya kara da cewa, "Irin wannan musaya wani nau'i ne na yin sulhu tsakanin gwamnati da 'yan tawaye a ko ina a duniya. Kuma ba a samun wata matsala idan an yi ta. Idan ka duba kasashe irinsu Colombia da Congo da kuma Kenya duk an yi irin wannan musaya, inda aka saki kwamandojin 'yan tawaye su kuma suka daina tayar da kayar baya."


Yadda aka karɓo 'yan matan

Hakkin mallakar hoto Twitter/ICRC_Africa
Image caption Kungiyar agaji ta ICRC ce ta shiga tsakanin gwamnati da 'yan Boko Haram

Wata majiya mai kusanci da yadda yarjejeniyar ta faru ta shaida wa BBC:

An ga wasu motocin kungiyar bayar da agaji ta Red Cross sun shiga jeji a kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Daga nan kuma jiragen yaki biyu da kuma sojoji ta kasa suka yi musu rakiya. Kuma an ga wasu mutum biyu fuskarsu a rufe.

Daga bisani ne aka dauki 'yan matan zuwa birnin Maiduguri, a kan hanyarsu ta zuwa Abuja.


Mai yin sharhi kan sha'anin na tsaro ya ce gwamnatin Najeriya da 'yan kungiyar Boko Haram sun gaji da yin fito-na-fito shi ya sa suke neman hanyar yin sulhu.

A watan Oktoban 2016 ma, kungiyar Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok 21 daga cikin 217 da ke hannunta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sace 'yan matan ya janyo zanga-zanga a duk fadin duniya
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An saki wasu 'yan matan 21 a watan Oktoba

Sai dai a wancan lokacin gwamnati ba ta bayyana cewa ta yi musayarsu da wasu dakarun Boko Haram ba, ko da yake wasu majiyoyi na cewa an yi hakan.

Malam Kabiru Adamu ya ce shigar da kungiyoyin kasashen waje da ma wasu kasashe cikin lamarin ya nuna cewa da wahala a fuskanci wata matsala daga baya.

Ya ce "Wannan musaya za ta taimaka wajen ci gaba da yunkurin da ake yi na samun dawwamammen zaman lafiya a Najeriya, kuma hakan zai sa a sako wasu mutanen da kungiyar take tsare da su wadanda ba 'yan Chibok ba ne."

A ganin masanin, dole Boko Haram ta yarda da irin wannan sulhu ganin cewa sojoji sun ci karfinta kuma ita kanta ma ta dare gida biyu, inda kowanne bangare ke son kawar da dan uwansa.

A daidai lokacin da iyalai da kuma masu fafutikar ganin an sako 'yan matan ke ci gaba da murna, babu shakka wannan ce-ce-ku-cen zai ci gaba da mamaye wannan yarjejeniya da aka kulla.

Labarai masu alaka