Na fi son zama a hannun Boko Haram— 'Yar Chibok

Wasu daga cikin 'yan matan Chibok 82 da aka sako Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kai 'yan matan 82 zuwa Abuja domin ganawa da Shugaba President Muhammadu Buhari bayan an kubutar da su ranar Lahadi

A Najeriya, daya daga cikin 'yan matan Chibok da Boko Haram ta sace ta ƙi amincewa a sako ta inda ta ce ta fi son ta ci gaba da zama tare da mijinta.

Har yanzu dai 'yan matan da aka ceto ba su samu sun gana da mahaifansu ba, sai dai mai magana da yawun shugaban ƙasa, Malam Garba Shehu ya ce a ranar Laraba ne za a fara shirin sada 'yan matan da Iyayensu.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tun da farko an shirya za'a saki yan mata 83 ne a musaya da 'yan kungiyar inda Boko Haram ta saki 'yan matan Chibok 82, yayin da ita kuma ta miƙawa ƙungiyar wasu dakarunta da ake tsare da su.

'Yan matan 82 da aka sako na cikin mata 276 da Boko Haram ta sace a watan Afrilun 2014, lamarin da ya jawo wa gwamnatin wancan lokacin kakkausar suka daga duk fadin duniya.

Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa: "An yi wata da watanni ana tattaunawa tsakanin gwamnati da shugabannin Boko Haram tare da gudunmawar ƙungiyoyi daban-daban da kuma ƙasar Switzerland.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Iyaye na jira su ga ko akwai 'ya 'yan su a cikin 'yan matan da aka gano

Ana kyautata zaton har yanzu mayakan Boko Haram na tsare da fiye da 'yan mata 100 daga cikin yan matan sakandaren Chibok, baya ga wasu maza da mata da mayaƙan ƙungiyar suka sace a shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Labarai masu alaka