Likimo nake yi ba bacci ba — Shugaba Robert Mugabe

Zimbabwe President Robert Mugabe (R) attending a State Dinner for the Africa-France Summit with the Rwandan president in Bamako on January 13, 2017. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Robert Mugabe 'likimo yake yawan yi ba bacci ba'

Mai magana da yawun Shugaban Zimbabwe ya yi karin haske kan yadda shugaban ke yawan rufe idanunsa na tsawon lokaci a wuraren taro, yana mai cewa likimo yake ba bacci ba.

Jaridar gwamnati ta Herald ta ambato George Charamba yana cewa, "Shugaban ba zai iya jure wa haske ba".

A yanzu haka shugaban na kasar Singapore inda ake duba lafiyar idanunsa.

Mista Mugabe, mai shekara 93, na da niyyar sake tsaya wa takarar shugaban kasar ta Zimbabwe a badi.

Labarai masu alaka