Amurka ta ce ta kashe shugaban kungiyar IS a Afghanistan

Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun Afghanistan da na Amurka ke mara wa baya sun sha kai farmaki kan mayakan na IS

Dakarun Amurka sun tabbatar da cewa an hallaka shugaban kungiyar IS a Afghanistan Abdel Hasib yayin wani samame da suka kai a ƙarshen watan Maris.

Sun ce Abdel Hasib ya mutu kwana goma da ta wuce a samamen da haɗin gwiwar dakarun Amurka da Afghanistan suka kai a gabashin kasar.

Ana dai zargin Mr Hasib da hannu a kai farmaki kan babban asibitin sojoji na birnin Kabul a cikin watan Maris, wanda ya hallaka fiye da mutum hamsin.

A cikin watan Afrilu ne rundunar sojin Amurka ta jefa wani bam mafi girma da ta taba amfani da shi a duk wani yaƙi, kan wasu hanyoyin karkashin kasa da aka yi amanna cewa mayakan IS ne ke amfani da su a Nangarhar.

Image caption Kungiyar IS ta kaddamar da hare-hare da dama a birnin Kabul

Kungiyar ta IS ta sanar da cewa za ta shiga cikin ƙasashen Afghanistan da Pakistan, a duk lokacin da ta ayyana lardin da ta kira Khorasan shekara ta 2015, kuma tuni ta kai hare-hare da dama.

A cikin watan Yuli ne wani harin bam a kan wani taron gangami a birnin Kabul ya hallaka mutum 80.

Wata uku bayan nan ne, aka sake kai irin wannan hare-hare lokacin bikin Ashura da a hallaka mutum 30, kuma a cikin watan Nuwambar shekara ta 2016 harin da aka kai a wani masallaci a birnin Kabul ya kashe fiye da mutum 30.

Kungiyar ta IS ta kuma yi ikirarin kaddamar da harin kunar bakin wake a Kotun Kolin birnin Kabul a watan Fabrairu da ya hallaka mutum 22.

Labarai masu alaka