Macron ya zama shugaban kasar Faransa

Kasar Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Emmanuel Macron ya kayar da abokiyar hamayyarsa Marine Le Pen a zaben shugaban kasar Faransa

Mr Emmanuel Macron ɗan takara mai matsakaicin ra'ayi, shi ne ya lashe zaɓen shugaban kasar Faransa, zagaye na biyu da aka gudanar.

Mai shekaru 39, Macron ya kayar da abokiyar hamayyarsa, Marine Le Pen.

Zai kasance shugaban kasar Faransa mafi karancin shekaru da aka taba samu, kuma na farko aka taba zaɓa ba daga manyan jam'iyyun ƙasar biyu ba.

Sakamakon zaben da aka gudanar dai ya nuna Mista Macron mai matsakaicin ra'ayi, ya samu sama da kashi sittin da biyar na kuri'un da aka kada, inda ya shiga gaban Marine Le Pen mai ra'ayin rikau, wadda ta samu kashi talatin da biyar na kuri'un.

Ms Le Pen din dai ta taya sabon shugaban murna, jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben.

Sai dai kuma ta ce yanzu jam'iyyarta ta National Front ita ce babbar jam'iyar adawa, kuma Faransa ta kasu gida biyu a siyasance, tsakanin masu kishin kasa da kuma masu rajin bin tafarkin manufofin kasashen waje.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban magoya bayan Mr Macron sun hallara a Louvre suna gangamin murnar samun galabarsa

An dan samu wata arangama a wani yankin na birnin Paris, lokacin da 'yan sanda suka harba hayaki mai sa hawaye kan taron daruruwan wasu masu zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben.

Dubban magoya bayan Mista Macron na ci gaba da murna a tsakiyar Paris, inda suke ɗaga tutoci.

Sabon zababben shugaban Mr Macron, na da jan aiki a gabansa, musamman ma in ana batun fadada ayyukan da suka shafi jama'ar kasar.

Zai kuma kafa sabuwar gwamnati, ba tare da zababbun wakilai a majalisar dokoki daga jam'iyyarsa ba.

Wani babban kalubalen kuma shi ne na zaben 'yan majalisar dokoki da aka shirya gudanarwa a cikin watan Yuni.

A ranar Lahadi mai zuwa ne ake sa ran Mr Macron za karbi ragamar mulki daga hannun shugaba Francois Hollande, wanda tuni ya taya shi murnar samun galaba.

Labarai masu alaka