Kun san 'yan matan Chibok din da aka ceto?

Chibok Girls Hakkin mallakar hoto Nigerian government

Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya wallafa sunayen 'yan mata 82 na makarantar sakandaren Chibok wadanda aka karbo a hannun kungiyar Boko Haram a ranar Lahadi, a shafinsa na Twitter.

Kungiyar ta sako 'yan matan ne bayan da gwamnati ta cimma yarjejeniya da ita, inda aka sakar mata wasu daga cikin magoya bayanta, ita kuma ta sako 'yan matan.

Ga dai jerin sunayensu kamar haka:

1. Kwatah Simon

2. Grace Dauda

3. Jummai Paul

4. Tabita Pogo

5. Yanke Shetima

6. Jummai Miutah

7. Juliana Yakubu

8. Mary Yakubu

9. Rulh Kolo

10. Mairama Yahaya

11. Racheal Nkeke

12. Fibi Haruna

13. Asabe Manu

14. Eslher Usman

15. Filo Dauda

16. Awa Ababa

17. Lydia Joshua

18. Na Oni Bitrus

19. Marlha James

20. Palmata Musa

21. Aisha Ezekiel

22. Mwada Baba

23. Hannatu Ishaku

24. Mwa Daniel

25. Rifkafu Soliman

26. Maryamu Yakubu

27. Rebecca Joseph

28. Ladi Audu

29. Amina Pagu

30. Sarah Nkeki

31. Esther Joshua

32. Saraya Yanga

33. Ruth Amos

34. Hauwa Musa

35. Hauwa Ishaya

36. Glory Aji

37. Mary Ali

38. Rahilla Bitrus

39. Luggwa Mutah

40. Lataba Maman

41. Lydia Habila

42. Deborah Peter

43. Naomi Yaga

44. Kwajigu Haman

45. Lugguwa Samuel

46.Maryamu Lawan

47.Tabita Hellapa

48. Ruth Ishaku

49. Maryamu Musa

50. Magaret Yama

51. Kauna Lalai

52. Solomi Tacitus

53. Naomi Yahona

54. Maimuna Usman

55.Grace Paul

56.Hauwa Ntakai

57.Yana Joshua

58. Comfort Bulus

59. Ramatu Yaga

60. Rhoda Peter

61. Naomi luka

62. Naomi Adamu

63. Iyatu Habila

64. Victoria wullgam

65. Ladi Ibrahim

66. Christiana Ali

67. Hanatu Stephen

68. Patina Fagbi

69. Martha James Bello

70. Tabita Silas

71. Yana Bukar

72. Abigail Bukar

73. Hadiza Yakubu

74. Naomi Zakariya

75. Maryamu wavi

76. Amina Bilama

77. Asabe Lawan

78. Mary Dauda

79. Maryamu Bilama

80. Naomi Filiman

81. Saratu Ayuba

82. Awa Yirma.

A lokacin da yake ganawa da 'yan matan, Shugaba Buhari ya bayyana sakin 'yan matan da cewa tamkar kyauta ce ga 'yan Najeriya ta cika shekara biyu a kan mulki da ya yi.

Mai magana da yawun Shugaba Buharin ya ambato shugaban na cewa, "A madadin dukkan 'yan Najeriya, zan so na bayyana muku farin cikin da nake ciki, da iyayenku da 'yan uwanku da kuma gwamnatin jihar Borno don samun 'yancinku."

A ranar Litinin ce za a bai wa iyayen yaran hotunansu don su gane 'ya'yan nasu, kafin a ba su damar ganawa da su ranar Talata a Abuja.

Labarai masu alaka