Wacce rawa Osinbajo zai taka a karo na biyu a matsayin muƙaddashi?

Shugaba Buhari da shugabannin majalisa a daren da zai tafi London Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaba Buhari da shugabannin majalisa a daren da zai tafi London

A karo na biyu a cikin wannan shekarar shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya sake tafiya birnin London don a sake duba lafiyarsa.

Dama dai yanayin lafiyarsa ya zama wani babban abin damuwa a kasar, inda ake cike da tsoron samun gibi a wajen jagorancin kasar zai iya shafar farfadowarta daga matsin tattalin arzikin da take fuskanta.

Amma a cikin sakon da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ya ce, ka da 'yan kasar su tayar da hankalinsu.

Kafin shugaba Buhari ya bar kasar ya gana da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki da Kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara. Haka kuma sai da aka aika wasika zuwa majalisar dokokin kasar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

Sashe na 145 (1) na Kundin tsarin mulkin ya ce, "A duk lokacin da shugaban kasa ya aika wa shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai wasika cewa zai tafi hutu ko kuma wani dalili zai sa ba zai iya zuwa ofis ba, to mataimakin shugaban kasa ne zai ci gaba da jan ragamar kasar, har sai lokacin da shugaban da kansa ya sake aika wata wasikar da zai bukaci a janye hakan."

'Yan Najeriya suna nuna matukar damuwa kan rashin lafiyar shugaban bisa fargabar kada a maimaita irin abin da ya faru a shekarar 2009 a lokacin da marigayi shugaba Umaru Musa 'Yar'adua ya yi ta fama da rashin lafiya, al'amarin da har ya sa aka kai shi kasashen Saudiyya da Jamus don neman magani.

Kuma saboda bai mika ragamar mulki ga mataimakinsa ba da kuma rashin bayyanawa 'yan kasar halin da yake ciki hakan ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a kasar. Shugaba 'Yar adua ya rasu a watan Mayun 2010 a sanadiyyar rashin lafiyar.

Sai dai a nasa bangaren a ranar Lahadi da daddare, shugaba Buhari ya mika ragamar mulkin kasar ga mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, kamar dai yadda ya yi lokacin da ya tafi hutun jinya a watan Janairu, inda ya shafe tsawon mako bakwai.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar a ranar Lahadi kan tafiyar tasa ba ta fadi tsawon lokacin da zai shafe a London din ba, "Likitoci ne za su fadi iya lokacin da zai shafe a can."

Amma ta kara da cewa, "Za a ci gaba da tafiyar da al'amuran gwamnati kamar yada aka saba, karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa."

A wancan lokaci dai Mista Osinbajo ya samu yabo ta bangarori da dama saboda 'yadda ya tafiyar da mulkin kasar' a matsayinsa na mukaddashin shugaban kasa.

Matakan da Osinbajo ya dauka na gaggawa wurin tunkarar matsalolin da kasar ke fuskanta bayan tafiyar Shugaba Buhari hutun jinyar na farko, sun bai wa masu sharhi mamaki.

Kuma hakan ya sa wasu ke ganin ya yi wa mai gidan nasa zarra a wata dayan da ya shafe yana lura da al'amuran kasar.

Sai dai fadar gwamnatin kasar ta ce duk wani yunkuri na nuna cewa Osinbajo ya fi Buhari "kokari ne na kawo rudani".

Duk da tsokacin da fadar shugaban kasar ta yi kan wannan batu, bai sa wasu 'yan kasar sun yi shiru ba, musamman game da matakin da babban bankin kasar CBN ya dauka na rage farashin dalar Amurkar da yake sayar wa mutane daga N375 zuwa N360.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Da yawa na ganin babu jituwa tsakanin mataimakin shugaban kasa da na hannun damar shugaban

Wani mai sharhi kan al'amuran siyasa a Najeriya Bashir Baba, ya ce tun a wancan karon bai kamata mutane su fara tunanin cewa Shugaba Buhari ya gaza yin wasu abubuwa ba har sai da ya bai wa mataimakinsa ikon jan ragamar mulki.

"Kamata ya yi mutane su fara tunanin cewa kafin shugaban ya tafi ya yi shimfidar fara ayyukan da suke ganin mataimakin shugaban ya cimma, don haka shi Farfesa Yemi karasawa kawai ya yi.

"Me ya sa ba su kalli lamarin ta haka ba? Ai ba a fadi wani sabon abu da za a ce mataimakin shugaban kasa ne ya kirkiro ba, kawai dai an ga abubuwa suna yin kyau ne, wadanda dama can an san shugaban kasar na yin aiki a kansu."

Bashir Baba ya kara da bayar da misali da cewa, "Gwamnatin Goodluck Jonathan na yawan cewa duk wani abu da wannan gwamnati ta cimma kokarinsu ne, don su suka yi shimfidar abin kafin daga bisani wannan gwamnatin ta zo ta ci gaba a kai, wanda ba lallai ba ne hakan.

"Don haka idan har mutane za su iya kawo misalin wani abu da za a ce Farfesa Osinbajo ne ya kirkiro shi, ya kuma aiwatar da shi, to a nan kam ba musu sai a ce kokarinsa ne shi kadai, amma ni ban san wani abu takamaimai da za a ce mataimakin shugaban ne ya yi wanda Buhari ya kasa yi ba."

Shi ma Dakta Hussaini Abdu wani mai sharhi kan al'amuran siyasa cewa ya yi, bai ga wani dalili na kawo rudani ko ce-ce-ku-ce kan dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu ba, don kuwa shugaban kasa da mataimakinsa ba su bayar da wata hanya da za a shiga tsakaninsu ba.

"Sam-sam babu wata alamar da sabani tsakaninsu, mataimakin shugaban kasa ya sha cewa ba ya aiwatar da komai sai ya gayawa shugaban kasa, komai yana yi ne da shawararsa.

"Shi kuma shugaban kasar ya sha fadin cewa mataimakin nasa ya yi duk abin da ya dace," in ji Dakta Abdu.

Ya za ta kaya a wannan karo?

Ganin cewa a karo na biyu Shugaba Buhari ya kara mika ragamar gwamnatin kasar ga mataimakinsa Farfesa Osinbajo, abin da mutane da dama za su so su gani shi ne ko mutanen da aka fi sani da na hannun-daman shugaban kasar za su bai wa mataimakin Ubangidan nasu hadin kai don tafiyar da al'amura yadda ya kamata?

Mista Bashir Baba ya ce abin da fi kamata shi ne su ba shi hadin kai don kyautatuwar al'amura kamar yadda Shugaba Buharin ya bukata.

"Ai a yanzu Osinbajo shi ne wuka shi ne nama, idan ya ga cewa akwai wanda zai kawo masa karan tsaye, ai sauran dabara ta rage ga mai shiga rijiya, shi ya san yadda zai yi.

"Yana da dukkan damar da zai yi maganin abin da zai kawo masa cikas, tun da shi ne mukaddashin shugaban kasa a yanzu," a cewar Malam Bashir.

Hakkin mallakar hoto Nigerian Government
Image caption Shugaba Buhari yana sallama da wasu na hannun damansa

'A rage ce-ce-ku-ce'

Babban jagoran jam'iyyar APC kuma tsohon gwamnan Lagos Bola Ahmed Tinubu a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi gabanin tafiyar shugaban ya ce, bai kamata 'yan Najeriya su dinga nuna fargaba da shakku a kan batun lafiyar shugaban kasar ba, wanda hakan zai iya rushe muhimman abubuwan ci gaban da ya sa a gaba.

Ya ce, "Shugaban kasa ya yi abin da ya kamata na bai wa mataimakinsa ragamar mulkin, kuma fahimtar da ke tsakaninsu su biyun ta kyautata al'amura da yawa."

Kiran na Mista Tinubu na zuwa ne saboda yadda 'yan kasar da dama ke kara nuna damuwa kan rashin lafiyar shugaban.

"Mun zabi Shugaba Buhari ne saboda mun yarda da gaskiyarsa, in dai har mun yarda cewa zai iya gyara al'amura a kasar nan, to ya kamata mu yarda da shi a akan duk wani mataki da ya dauka da ya shafi lafiyarsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu ya ce bai kamata a irin wannan lokaci 'yan Najeriya su yi ta ce-ce-ku-ce kan lafiyar Shugaba Buhari ba

"Buharin da na sani mai gaskiya ne da rikon amana."

'Yan Najeriya da dama dai na ci gaba da bayyana damuwarsu kan wannan tafiya ta shugaba Buhari, inda masoyansa ke cewa tafiyar tasa ta dace don sai da lafiya ne zai iya yin mulkin da cika alkawuran da ya dauka.

Suna masa fatan ya samu sauki ya dawo ya ci gaba daga inda ya tsaya.

Wasu kuwa gani suke gara ya yarda kwallon mangwaro ya huta da kuda, wato ya bar mulkin ya mayar da hankali kan neman lafiyarsa.

Fargaba kan yanayin lafiyar shugaba Buhari ta kara ta'azzara ne bayan da aka ga bai halarci taron majalisar ministoci sau uku a jere ba, inda kungiyoyin fararen hula suka dinga kiransa da ya koma London don a sake duba shi.

Amma bayyanarsa a masallacin Juma'a a makon da ya gabata, wadda ita ce ta farko a cikin mako biyu, ta dan kwantar da hankalin masoyansa.

Sai dai jami'an fadar gwamnati sun ce hutawa yake yi kuma yana aiki ne daga gida, yayin da ita ma mai dakinsa Aisha Buhari ta ce ana zuzuta rashin lafiyar mijin nata.

A wannan karon dai a iya cewa za a zura ido ne don ganin ya ya mukaddashin shugaban kasar zai tafiyar da ragamar mulkin da aka damka masa da kuma yadda za ta kaya a tsakaninsa da na hannun-dama shugaba Buhari, sannan kuma ko yaushe ne shugaban zai dawo kasar.

Labarai masu alaka