Kun san Shugabannin duniya masu ƙarancin shekaru?

Emmanuel Macron Hakkin mallakar hoto ERIC FEFERBERG
Image caption Mista Macron ne shugaba mafi kankantan sheraru a Faransa.

Emmanuel Macron mai shekara 39 ne shugaba mafi karancin shekaru a tarihin kasar Faransa.

Zabensa da aka yi a matsayin shuganban kasa ya kafa tarihi inda ya fi Louis-Napoleon Bonaparte, wanda ya hau mulki yana shekara 40 cikin shekara ta 1848.

A nan, za mu duba wasu daga cikin shugabanni masu karancin shekaru a duniya.

Ta Farko, Shugabar San Marino,Vanessa D'Ambrosio

Hakkin mallakar hoto Vanessa D'Ambrosio
Image caption Vanessa D'Ambrosio ce shugaba mafi kankantan shekaru a duniya.

Vanessa D'Ambrosio mai shekara 29 ce shugabar kasa mafi karancin shekaru a duniya, wadda ta shugabanci kasa mafi karanta a duniya, wato San Marino.

Kasar tana kewaye da Italiya, inda mazauna kasar suka kai sama da 33,000.

Na biyu,Shugaban Koriya ta Arewa,Kim Jong-un

Hakkin mallakar hoto STR
Image caption Kim Jong-un ne shugaba mafi kankanta shekaru na biyu a duniya

Kim Jong-un mai shekara 34 ne shugaban Koriya ta Arewa, duk da cewa ba matashin da ake goyon bayansa ba ne, shi ne shugaba na biyu mafi karancin shekaru a duniya.

Ya kasance a kan mulki tun shekara 2012, inda yake kula da ci gaban makaman nukuliya da makamai masu linzami.

Na Uku,Firai ministan Estonia, Juri Ratas

Hakkin mallakar hoto THIERRY CHARLIER
Image caption Juri Ratas ne firayam ministar kasar Estonia

Kasar Estonia wadda ke karkashin tsohuwar Tarayyar Sobiyet ta zabi gwamnatin da ke karkashin jagorancin firai ministan kasar, Juri Ratas a shekara ta 2016.

Firai ministan, mai shekara 38 ya yi suna a jihar Baltic, inda marasa rinjaye masu amfani da harshen Rasha ke da zama.

Na hudu, Firai ministan Ukraine,Volodymyr Groysman

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Volodymyr Groysman ne firai minista mafi kankntar shekaru a Ukraine

Volodymyr Groysman dan shekara 38 ne da aka zabe shi firai ministan Ukraine a shekara ta 2016.

Duk da cewa, shugaba Petro Poroshenko ke da iko a kasa ta biyu mafi girma a Turai, Mista Groysman ne firai minista mafi karanci shekaru na biyu a tarihin kasar.

Yana da ra'ayin mazan jiya inda yake goyon bayan Ukraine ta shiga kungiyar Tarayyar Turai da Nato amma ba ya goyon bayan auren jinsi.

Na biyar, Sarkin Bhutan,Jigme Khesar Namgyel Wangchuck

Hakkin mallakar hoto HO
Image caption Sarkin Jigme Khesar Namgyel Wangchuck da Jigme Singye Wangchuck tare da yarsu HRH Gyalsey Jigme Namgyel

Idan aka yi batun masarauta kuwa, kamata ya yi a ambaci sunan Sarkin Bhutan, Jigme Khesar Namgyel Wangchuck mai shekara 37.

Ya hau mulki tun shekara ta 2006, yana kuma goyon bayan kasar ta sake tsasin mulkinta zuma mulkin dimokradiyya.

Na shida, Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani

Hakkin mallakar hoto DANIEL IRUNGU

Sarki Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, ya hau karagar mulki a matsayin sarkin Qatar a shekara 2013 bayan da mahaifinsa ya rasu.

Ya yi karatu a makarantar horar da sojoji a Birtaniya.

Sarkin mai shekara 36 ne mataimakin kwamandan sojoji da kuma shugaban kwamitin wasannin Olympic.

Sarki Hamad Al Thani ya taka muhimmiyar rawa ga samarwa kasarsa damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta Fifa a shekara 2022.

Qatar, na daya daga cikin kasashen da basu kwari a cikin wasan Gulf, a yanzu tana daya daga cikin kasa mafi arziki amma kungiyoyin kare hakkin bil'adama na ci gaba da sukarsa kan yadda ba ya kare hakkin bakin haure.

Sai kuma tsofaffin shugabannin,Robert Mugabe na Zimbabwe

Hakkin mallakar hoto Reuters

A wani bangare daban, shugaban Zimbabwe Robert Mugabe mai shekara 93 ne shugaban kasa da yafi kowa dadewa a kan mulki a duniya.

Mista Mugabe ya yi suna a lokacin yakin sojoji a shekara 1970 da yake yaki da fararen fata marasa rinjaye masu mulki domin al'ummar kasar su samu 'yancin kansu.

Amma ana sukarsa cewa a mulkinsa, yana kokarin kawar da abokan hamayyar siyasa da kuma magudin zabe.