Musayar 'yan matan Chibok kuskure ne — PDP

PDP
Image caption PDP na fargabar sulhun da ake yi da 'yan Boko-Haram

Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya bangaren Ahmad Makarfi, ta yi Allah-wa-dai da musanyar mayakan Boko Haram da 'yan matan Chibok da gwamnatin kasar ta yi.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Jam'iyyar, Dayo Adeyeye ya fitar ya ce, jam'iyyar ta bayyana ceto 'yan matan Chibok 82 a matsayin wani gagarumin ci gaba. Ta ce, kame da tsare yaran da kungiyar Boko Haram ta yi, a shekara ukun da ta gabata ya haifar da dimuwa ga iyalai da mutanen kasar da ma kasashen waje.

"Amma babban abun dubawa a nan shi ne hanyar da aka bi ta musanyar 'yan matan, abin da rahotonni ke cewa shi ne an saki 'yan matan ne bayan da aka saki mayakan kungiyar da ke hannun gwamnati, idan dai hakan ta tabbata to wannan babban kuskure ne gwamnati ta tabka," in ji sanarwar.

Ta kara da cewa, "'Yan ta'addan da aka yi wannan musanyar da su kenan sun tsallake doka, kuma duk wani yunkuri da jami'an tsaro ke yi na hukunta su ya tashi a banza kenan."

Jam'iyyar ta kara da cewa, "Sulhun ya sabawa dokokin duniya na cewa ba a yin sulhu da ta'addanci, "sakin mayakan kamar karin kaimi ne ga ayyukan ta'addanci a kasar. Sakinsu zai kara jefa al'umma cikin fargabar karuwar hare-hare."

Jam'iyyar na ganin 'yan kungiyar za su ci gaba da garkuwa da mutane da tsare su da nufin cewa gwamnati ta yi musayarsu da mayakan kungiyar da ke hannuta.

Ta kuma sakin wasu daga cikin 'yan matan zai kara haifar da fargaba a zukatan iyalan wadanda ba a saki 'ya'yansu ba. "Da ya kamata a ce duka 'yan matan aka saki ba wasu daga cikinsu ba."

Sai dai kuma PDPn ta ce ta yaba da kokarin da shugaban kasa ya yi na ganin cewa an saki 'yan matan, "kuma muna fatan za a gaggauta mika su ga iyalasu a kan lokaci."

Ta kuma taya 'yan matan da iyayensu murna, sannan kuma ta yi fatan cewa sauran 'yan uwansu za su kubuta nan ba da dadewa ba.

Amma a yayin da jam'iyyar PDP ke sukar wannan mataki, su kuwa kungiyoyin fararen hula na gida da waje kamar Amnesty International da BringBackOurGirls maraba suke da wannan yunkuri.

Labarai masu alaka