Wanene sabon shugaban kasar Faransa Macron?

poster of Macron Hakkin mallakar hoto Getty Images

Wani abu game da Emmanuel Macron shi ne, yana yi wa mutane da dama kwarjini.

A yakin neman zaben makon jiya, yayi magana da shugaban kungiyar CGT a wata masanantar dake arewacin kasar da za a rufe nan ba da jimawa ba. Wadannan matasa suna tsani manufofinsa. Ayyukan yinsu za su koma kasar Poland.

Amma duk da haka sun saurare shi cikin natsuwa.

Wataran kuma yana iya gabatar da jawabi ga manyan mutane da ma matasa masu tashen gayu. Kuma su kan bashi hadin kai su saurari shi duk da basu sonshi.

A wani shirin talabijin da aka yi kan sabon shugaban Faransan: wani ya ce, shugaban zai iya jan hankalin kujerar ofishinshi.

Koma dai mai su ke tunani kan siyasarsa, kasar Faransa ta riga zabi mafi basira a zamninsa. Tabbas yana da kwarjini, har'ila yau kuma ga kaifin tunani, yana kuma da kwazo da basira, matashi ne mai kyakyawan fata wanda bai yadda da cin hanci ba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Emmanuel Macron ya yi amfani da karfin ikonsa na iya shawo kan mutane a lokacin yakin neman zabensa

A duk lokacin da ka saurari jawabin Macron, sai kaji ka gamsu da maganarsa. Mutane kan yi mamakin abubuwan da yake fada. Bututwan da yake magana a kansu duk haka suke. Amma me yasa ba mu yi tunanin haka a baya ba.

Ko zai cigaba da jan hankali

Kai! amma akwai gogayya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Macro ya auri malamarsa Brigitte Trogneux, wacce ta girmeshi da shekara 24

Ya auri Brigitte Trogneu, malamarsa ,wacce ta girmesa da shekara 24.

Yanzu yana da shekara 39, duk da cewa ba shi da gogewa a harkokkin siyasa, amma yana matsayin shugaban kasar da ita ce ta biyar a kasashen a duniya.

Shin akwai wanda zai ga laifinshi idan ya naji kamar a kwai wanda ke idon kansa?

Zaben sabon shugaban kasar ba shi ne lokacin da ya jawo mutane suka nuna suna sonshi ba, kuma yawancin mutane za suyi fatan alkhairi ga mutumin da yake nagari mai kyakkyawar dabi'a, domin suna bukatar wanda zai sadaukar da kanshi ga kasar.

Sai dai idan akwai wata ayar tambaya akan Emmanuel Macron, to ba zai wuce wasu abubuwa na musamman da suke tattare da shi ba.

Baiwarsa ta iya magana ( ka tuna cewa iya maganarsa da kwaikwayo a aji ne yasa suka fara son juna shi da Brigitte).

Sai dai sau da yawa abin da yake sawa jama'a fargaba da Macron shi ne kalmomin da yake amfani da su, sune su ke yi masa aikinsa.

Furuci ne da suke dinke baraka, da furucin kuma suke tausasa abokan adawarsa.

A lokacin yakin neman zabe, sau da yawa yana hada amsoshinsa da kalmomin en meme temps "a lokaci guda" inda hakan ya zama abin zolaye a tsakanin 'yan jarida.

Karin bayani