Ana zaben shugaban kasa a Koriya ta Kudu

'Yan takara 13 ne ke fafata wa a zaben shugaban kasar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan takara 13 ne ke fafata wa a zaben shugaban kasar

Al'ummar kasar Koriya ta Kudu na zaben shugaban kasar don maye gurbin Park Geun-hye, wacce aka tsigeta aka kuma tsare ta bisa zargin aikata almundahana.

'Yan takara 13 ne dai ke fafata wa a zaben, a dai dai lokacin da hankulan kasashen duniya suka karkata ga yanayin da ake cikin yankin sakamakon zaman dar dar ake yi yayin da Amurka da Koriya ta arewa ke ci gaba da yiwa juna barazana kan makaman nukiliya.

Za dai a gudanar da zaben ne ba kamar yadda aka tsara ba tun da farko saboda gibin da aka samu bayan tsige shugabar kasar sakamakon aikata cin hanci.

Duk dai wanda zai kasance sabon shugaban kasar ta Koriya ta Kudu wajibi ne ya kasance ya samu mafi yawan kuri'u kasancewar ba'a tsara yin zabe zagaye na biyu ba na 'yan takara da suka fi yawan kuri'u a zagaye na farko.

Hankula dai sun fi karkata akan Moon Jae-in, dan takarar jam'iyyar masu sassaucin ra'ayi,wanda kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a suka nuna cewa shi ne zai lashe zaben.

A lokacin yakin neman zaben sa dai Mr Moon ya nuna cewa zai farfado da dangantaka tsakanin kasar da Koriya ta arewa sabanin tsarin yadda wasu shugabannin kasar na baya suka yi rika yi wadanda tare da kasar Amurka suka katse duk wata danganta tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa tare da sanya takunkumi masu tsauri ta fuskar tattalin arzikin.

Masu sharhi kan al'amurran yankin sun ce, ita kanta makwabciyar kasar wato Koriya ta arewa, a kaikaice ta nuna dan takaran da ta ke son ya lashe zaben, musamman bayan wani sharhi da jaridar da jam'iyya mai mulki ta wallafa dake nuna goyon baya ga dan takaran da zai farfado da dangantaka tsakanin Koriya ta Kudu data arewa.