Afirka Ta Kudu: Zakuna sun tsere sun shiga gari

Zakuna Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi ta amfani da helikwafta don gano inda zakunan suke

Hukumar gandun namun daji ta Afirka Ta Kudu ta yi kira ga mazauna yankin Komatipoort da ke daura da gandun dajin Mpumalanga da su lura da kyau wajen zirga-zirgarsu saboda tserewar da wasu zakuna biyar suka yi daga gandun namun daji na Kruger National Park.

An dai yi amanna zakunan suna ta walagigi a yankin da ke kusa da gandun namun dajin.

Sai dai hukumar gandun namun dajin ta ce tuni an gano wajen da zakunan suke a can kusa da kan iyakar kasar Swaziland.

An yi ta amfani da helikwafta don a gano inda zakunan suke.

A yanzu masu kula da gandun namun dajin suna kokarin kama su don harba musu allurar kashe jiki don su samu damar mayar da su cikin gandun.

Wakiliyar BBC a kasar ta ce mutane sun samu kwanciyar hankali sosai bayan da aka gano inda zakunan suke, kuma ba a samu rahoton cewa sun yi wa kowa illa ba.

Wani mazaunin yankin ya ce ya ga zakunan a ranar Litinin da daddare amma sa'arsa daya yana cikin mota ne ba da kafa yake tafiya ba.

Labarai masu alaka