Yaushe Majalisa za ta amince da kasafin kudin Nigeria?

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tun watan Disambar 2016 Shugaba Buhari ya mika kasafin kudin ga majalisa

A ranar Talata ne Majalisar dattawan Najeriya ta karbi rahoton kasafin kudin kasar na 2017 daga kwamitin tsare-tsare na kasafin.

Shugaban kwamitin tsare-tsaren kasafin Sanata Danjuma Goje ne ya gabatar da rahoton a zaman da majalisar ta yi.

'Yan majalisar dattawan sun tattauna sosai a kan rahoton an kuma yi masa gyare-gyaren da suka dace.

Shugaban Majalisar Sanata Bukola Saraki ya taya mambobin kwamitin murnar kammala hada rahoton tare da yi musu jinjina kan aikin da suka yi 'tukuru' a kan kasafin kudin.

Ya kuma ce za a gabatar da abin da kasafin kudin ya kunsa a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu a gaban Majalisar, inda za a raba takardun cikakken bayanin kasafin ga 'yan majalisar don kowa ya duba abin da ya kunsa.

Ya ce aikin da kwamitin ya yi a kan rahoton zai taimaka wajen gaggauta zartar da kudurin.

Majalisar ta ce a wannan karon za a fayyace dukkan abin da kasafin kudin ya kunsa, babu abin da za a boyewa al'ummar kasa.

Tun a watan Disambar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta gabatar da kasafin kudin ga majalisar dokokin amma sai a yanzu ne kwamitin da ke kula da hakan ya kammala hada rahotonsa.

A makon da ya gabata ne wa'adin kasafin kudin kasar na shekarar 2016 ya kare, amma majalisar ta ce kundin tsarin mulkin kasar ya amince da cewa gwamnati na iya ci gaba da kashe kudade har zuwa watan Yulin bana.

A don haka mahjalisar ta yi alkawarin kammala duba kasafin kudin da kuma amincewa da shi kafin watan Yulin.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudurin kasafin kudin na naira tirilyan 7.30 na shekarar 2017 ga majalisar ranar 14 ga watan Disambar 2016.

Daga bayanin kudurin kasafin kudin, naira tirilyan 2.24 wanda shi ne kashi 30.7 cikin 100 wajen gudanar da manyan ayyukan raya kasa, yayin da naira 2.98 kuma za a kashe su wajen gudanar da harkokin gwamnati na yau da kullum.

Labarai masu alaka