Inida: An daure alkali kan laifin raina kotu

Indiya Hakkin mallakar hoto Press Trust of India

A wani hukunci da ba kasafai ake yanke irinsa ba, kotun koli ta Indiya ta yanke wa wani Alkali na babbar kotu a Calcutta, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda laifin raina kotu.

Mai shari'a Chinnaswamy Swaminathan Karnan zai kasance na farko da ke aikin alkalanci da aka daure a tarihin kasar.

An sami Justice Karnan ne da laifin rubuta wasu wasiku inda ya yi wasu zarge-zarge kan wasu takwarorinsa alkalai.

Tun watanni da suka gabata, Justice Karnan ya sha samun takun saka tsakaninsa da alkalan manyan kotu.

Ya rubuta wasika a watan Janairu ga Firai ministan kasar Narendra Modi inda ya bayyana sunayen bara-gurbin alkalai 20 da ya ce suna cike da cin hanci da rashawa da kuma wasu manyan jami'an shari'a uku.

Sai dai ya gaza bayyana wata shaida kan hakan, amma ya bukaci Mista Modi da ya yi bincike kuma ya dauki mataki a kan hakan.

Bayan hakan ne kuma aka gayyace shi a gaban kotun koli aka kuma hana shi aiwatar da duk wani abu da ya shafi ayyukan shari'a.

Justice Karnan ya mayar da martani ta hanyar zargin alkalai bakwai da nuna wariya da hana su fita daga kasar da kuma neman diyya.

Daga nan ne sai alkalan kotun kolin suka bukaci Likitocin gwamnati da su binciki lafiyar kwakwalwarsa.

Wannan dai ya sake harzuka Mista Karnan ya shi ma ya sake mayar da martani cikin fushi ta hanyar ba da umarnin yin irin hakan ga wadancan alkalan bakwai.

A ranar Litinin ne kuma ya yankewa babban mai shari'ar Indiya da sauran alkalan bakwai hukuncin daurin shekara biyar a gidan yari.

Umarnin na cewa alkalan sun aikata laifin nuna bambanci da cin zarafi da sauran su.

A ranar Talata ne kuma kotun kolin ta haramtawa kafofin yada labari wallafa da watsa sanarwar da alkali Karnan ya fitar.

Labarai masu alaka