Ƙarancin abinci yana ƙara yin ƙamari a Nijar

Nijar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamnatin kasar ta yi aniyar magance matsalar

A jamhuriyar Nijar wasu 'yan majalisar dokoki da kungiyoyin kare hakin jama'a sun koka game da yadda suka ce matsalar karancin abinci ke dada kamari a wasu yankunan kasar musamman a karkara.

Lamarin ya ta'azara in ji su, ganin farashin cimakar na ci gaba da hauhawa a daidai lokacin da mazauna karkarar ke cikin kuncin fatara da talaucin.

Gwamnati dai ta tabbatar da matsalar inda ta kira wani taron abokan arzikinta a makon jiya domin su taimaka mata ta tunkari matsalar.

Daga Yamai wakilinmu BARO ARZIKA ya aiko da wannan rahoton:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Rahoton Karancin Abinci a Nijar

Labarai masu alaka