Kun san Matar shugaban Faransa sa'ar mahaifiyarsa ce?

Macron Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Brigitte tare da mijinta Emmanuel Macron

"Brigitte! Brigitte! Brigitte!" Yadda magoya baya suka dinga ihun kiran sunanta kenan a lokacin da ita da mijinta sabon shugaban Faransa Emmanuel Macron suka zo yin jawabi. Amma wace ce Brigitte?

Na farko: Nasu soyyayarsu ba irin wadda aka saba gani ba ce.

Akwai tazarar shekara 24 tsakaninsu, kamar irin ratann shekarun da ke tsakanin Donald and Melania Trump.

Emmanuel Macron mai shekara 39 da Brigitte Macron mai shekara 64 sun hadu a lokacin da take malamarsa mai koyar da darasin wasan kwaikwayo a makaranta.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Brigitte Macron na da yara uku da tsohon mijinta.

Misis Macron ta ce, ''Mista Macron a lokacin da yake da shekara 15, irin halayyar da yake bayyanawa sunfi shekarunsa. Dalibi ne a makarantar Jesuit dake Amiens, inda ta ce '' yana da dangantaka da wasu manya da dama maimakon ya nuna halayyar matashi.

Ta kara da cewa, ''Kwazonsa da iliminsa ne ya burgeni.''

Mijin Brigitte Trogneux na farko wani ma'aikacin banki ne André Auzière kuma ta haifi yara uku da shi.

Iyayen Mista Macron sun gano cewa ɗansu na son wata amma ba su san wace ce ya ke so ba.

Anne Fulda ya ruwaito cewa sun yi sammanin yana son 'yar MAlamar tasa ce Laurence Auzière wadda suke aji daya da shi a makaranta. Amma ashe uwa yake so ba 'yar ba.

A lokacin da iyayensa suka gano hakan, sun gaya mata cewa ta nisanci dansu har sai ya cika shekara 18, inda ita kuma ta ce ba zata iya yin wannan alkawari ba.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matar Mista Macron za ta yi aiki kafada da kafada da shi a fadar Élysée Palace

Kafin Mista Emmanuel ya samu shekara 17 ya gayawa Misis Brigitte zai aureta wata rana. Bayan shekara goma da yin hakan, a shekarar 2007 kuwa ya cika alkawarinsa.

A yanzu mahaifiyar Mista Macron ta ce tana ganin Brigitte a matsayin abokiyarta ba suruka ba.

Laurence 'yar ajin Mista Macron ta kasance shahararriyar mai goyon bayan mijin mahaifiyarta. Daya dan nata kuma Tiphaine mai shekara 32, lauya ne kuma shi ne mai kula da harkokin yakin neman zaben Mista Macron.

Ragowan dangin Macron sun kasance kusa da shi a lokacin bikin lashe zabe a ranar Lahadi a Louvre dake Paris.

Matar sabon shugaban tana da yara uku da ta haifawa tsohon mijinta da kuma jikoki bakwai

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Macron da ke aji daya da Laurence Auzière's ya zama mijin uwarta kuma shugaban Faransa

Misis Macron ta yi marabus a aikinta na koyarwa bayan mijinta ya zama ministan tattalin arziki, sai ta zama mai ba shi shawara.

Ana yaba mata kan jan hankalinsa da take yi na kulawa da batutuwan da suka shafi mata a harkokin siyasa.

Mista Macron ya yi alkawarin cewa rabin wadanda zasu tsaya takara a jam'iyyarsa ta En Marche a watan Yuni zuwa majalisar dokoki za su kasance mata.

Ya kara da cewa yana son shigar da tsarin ayyukan matar shugaban kasa cikin ayyukan gwamnati.

A wata hira da ya yi da Vanity Fair a watan da ta gabata, ya ce, ''Idan aka zabe ni, au ku gafarce ni, ina nufin idan aka zabe mu ni da ita, to za ta kasance a kusa da ni, tana ayyukanta da kuma ofishinta.''

A matsayinta na tsohowar malama, za ta taimaka wajen kula da matasa sosai.

Mista Macron ya ce ba za a biya ta albashi don wannan aikin ba. "Amma za a dinga shawarwari da ita don gudanar da wasu al'amura, za ta kasance tare da ni kamar yadda ta saba, kuma zata taka rawa a fanin siyasa."

Jaridun kasar sun yi ta wallafa labaran raha a kan ma'auratan, inda suke zana Mista Macron a matsayin dalibi yana daukar darasi a wajen Malamarsa.

Abokiyar takararsa Marine Le Pen ta taba yi masa habaici da cewa, "Mista Macron na ga kamar kana son ka yi min wasa kamar na Malama da dalibinta. Amma dai ni a wajena wannan bai shafe ni."

Ko ita da kanta Mista Macron ta kan yi wa bambancin shekarunsu dariya. An ambato ta a wani littafi tana cewa, "Yana bukatar yin takarar shugabancin kasa a shekarar 2017 saboda a shekarar 2022 babbar matsalarsa ba za ta wuce na kallon fuskata ba," (tana nufin a matsayin tsohuwa.)

Labarai masu alaka

Karin bayani

Labaran BBC