Ko Nigeria za ta iya yin koyi da India a harkar makamashi?

Wani mazaunin India Hakkin mallakar hoto URVASHI BACHANI
Image caption India ta kaddamar da katafaren gonar hasken rana mafi girma a duniya

India ta kaddamar da katafariyar cibiyar samar da lantarki ta hasken rana mafi girma a duniya a farkon wannan shekarar, kuma cibiyar ta nunka karfin aikin da take yi sau hudu a cikin shekara uku da ta gabata.

Hakan ya samarwa miliyoyin gidajen da ba sa samun wuta daga gwamnati wutar lantarki. Amma kuma wadanne abubuwan za a iya samar wa wadanda za su iya saka hasken solar ya maye gurbin makamashin wuta kamarsu gawayi da iskar gas?

Rameshwarlal Choudhary, wani manomi mai shekara 45 da matarsa Dakha mai shekara 40, suna zama tare da yaransu biyu a kusa da wata cibiyar Solar a kauyen da ke garin Rajasthan a kasar Indiya.

Gidansu na asabari ne mai dauke da rufi mara kauri, kuma gefe guda a bude yake ta yadda hasken solar din ke shiga sosai.

Har a cikin wata shidan da suka gabata, suna daga cikin kaso 44 cikin 100 na gidajen karkarar Indiya da basu da wutar lantarki.

A yanzu, sakamakon na'urar Solar da aka dora a kan wata bishiya a wajen gidan, suna samun wuta a fitulu uku da suke da su a gidansu. Daya a cikin gidan daya kuma a wajen gidan sannan dayan kuma a kan bishiya da ke hasko rufin gidan.

Hakkin mallakar hoto URVASHI BACHANI
Image caption Gonar sola mai samar da wutar lantarki da hasken rana ta kai eka 2,500

'Yarsu Pooja, daliba mai shekara 17 ta ce, "Muna iya kai wa har karfe 10 na dare muna karatu da rarar wutar da muke samu."

Kuma a karon farko iyayenta za su iya nome gonarsu kuma su tatso nonon shanu kafin rana ta fadi.

"Wutar kuma na taimakawa wajen kare mu daga macizai da beraye da kuma kunamai," a cewar Ramjilal yaronsu mai shekara 20 wanda shi ma dalibi ne.

A watan Nuwamba, kasar ta kaddamar da cibiyar wutar lantarki ta hasken rana mafi girma a duniya a Kamuthi da ke garin Tamil Nadu.

Cibiyar ta kai eka 2,500 kuma a kullum sai tawagar mutum-mutumi sun tsaftace na'urorin sola miliyan 2.5 wadanda suma suke amfani da hasken rana.

A yayin da kasashe kamar su Jamus da Burtaniya ke fuskantar karancin kafa sabbin na'urorin samar da wuta ta hanyar amfani da hasken rana sakamakon janye tallafi da gwamnatocinsu suka yi, na Indiya da China kuwa bunkasa suke yi.

Hakkin mallakar hoto ADANI GROUP
Image caption A shekarar 2010, gigawatts 50 kawai na sola aka dasa a duniya baki daya

A cikin shekara uku da ta gabata, Indiya ta nunka samar da wuta ta hasken rana zuwa ma'aunin wuta na gigawatts 12. Gigawatts 1 zai iya samar wa gidaje 725,000 wutar lantarki.

Wannan adadin zai kusa nunkawa a cikin wannan shekarar, inda Indiya ta kara gigawatts 10 a 2017 kuma suna sa ran gigwatss 20 nan gaba.

China ma tana dashen na'urorin solar kuma samar da wutar ya karu daga gigawatts 43 zuwa gigawatts 77 a shekarar da ta gabata.

A shekarar 2010, gigawatts 50 na sola kawai aka dasa a duniya baki daya.

"Dashen sola da aka yi ya wuce yawan yadda ake zato a shekaru kadan da suka gabata a cewar Josefin Berg, babbar mai sharhi a tawagar da ke bincike kan dashen sola na IHS.

Hakkin mallakar hoto MARKO HUTTULA
Image caption Kusan kashi 35 cikin 100 na hasken ranar da ya kamata a ce na'urorin na zukewa na ficewa

Babbar matsalar ita ce, kusan kashi 35 cikin 100 na hasken ranar da ya kamata a ce na'urorin na zukewa na ficewa ne maimakon a ce suna sarrafa shi zuwa wutar lantarki.

Wata tawagar bincike da ke Finland na kyautata zaton haka.

Farfesa Marko Huttula da Wei Cao da ke jami'ar Oulu sun yi nazari kan na'urori 32 domin gano hanya mafi inganci wajen samun haske.

Ya zuwa yanzu dai, sun yi nasara wajen rage kason hasken da ake asararsa daga kashi 35 cikin 100 zuwa kashi 12 cikin 100.

Hakkin mallakar hoto SMARTFLOWER
Image caption China ma tana dashen na'urorin solar kuma samar da wutar ya karu daga gigawatts 43 zuwa gigawatts 77 a shekarar da ta gabata

A cewarsu, rage hasken da ake asara ta wannan hanyar na karawa na'urorin sola din makamashi har zuwa kashi 17 cikin 100.

A yanzu suna kokari su bunkasa yadda ake aiwatarwa da hadin kan China.

Labarai masu alaka