Ana taro kan rikicin Somaliya a London

Shugaba Mohammed Farmajo na kokarin shawo kan mayakan Al-Shabab Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Mohammed Farmajo na kokarin shawo kan mayakan Al-Shabab

Shugabannin gwamnatoci da wakilan kungiyoyin a kasashe daban daban, za su hallara a Burtaniya domin halartar taro kan rikicin kasar Somalia da za'a fara ranar Laraba.

Shekara biyar ke nan da aka gudanar da irin wannan taron a birnin London da nufin nemo hanyoyin kawo karshen rikicin kasar.

Taron dai zai mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro da siyasa da kuma shirin sake gina kasar ta Somalia.

Wannan taron yana zuwa ne a dai-dai lokacin da sabuwar gwamnatin kasar ta shugaba Mohammed Farmajo ke kokarin shawo kan 'yan kungiyar Al-Shabaab.

A lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki a watan Fabrairu, shugaban Somaliya, Mohamed Abdullahi Farmajo, ya yi alkawarin inganta tsaro da kuma aiki domin samar da sulhu a kasar.

Masu sharhi sun ce sabuwar gwamnatin za ta fuskanci manyan kalubale a yayin da ya ke yakar ta'adancin kungiyar Al Shabaab, da matsanancin fari wanda ya sa kasar ta samu kanta a cikin bala'in yunwa.

Labarai masu alaka