US: An kori shugaban hukumar FBI

Ana kara samun suka dangane da matakin gwamnatin Amurka na korar Mr Comey Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana kara samun suka dangane da matakin gwamnatin Amurka na korar Mr Comey

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori shugaban hukumar binciken manyan laifuka ta kasar, wato FBI James Comey.

Fadar gwamnatin kasar ta ce, Mr Trump ya ce ana bukatar sabon shugabanci a hukumar domin maido mata da amincin da jama'a suke da shi a kan hukumar ta FBI .

Ana dai kara samun suka daga bangarori daban-daban game da korar shugaban hukumar ta FBI.

An dai mika masa takardar sallamar ne a lokacin da ya ke yiwa ma'aikatan hukumar jawabi a Los Angeles.

A cikin takardar,Mr Trump ya shaidawa Mr Comey cewa ya gaza a wajen bayar da shugabanci na gari, dan haka akwai bukatar wanda zai maye gurbinsa da zai dawo da martabar hukumar a idanun jama'a.

Mr Comey dai na jagorantar wani bincike da ke da alaka da yakin neman zaben Mr Trump da kuma Rasha.

To sai dai fadar gwamnatin Rasha ta ce an sallame shi ne saboda yadda ya ke aiki akan sakonnin emel din 'yar takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar Democratic da ta sha kayi, wato Hillary Clinton.

Labarai masu alaka