'Yar Majalisar da ke shayar da 'yarta a zauren majalisa

Sanata Larissa Waters Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sanata Larissa Waters tana shayar da jaririyarta Alia Joy.

Sanata Larissa Waters, ta kasar Australiya ta zama mace ta farko da ta shayar da 'yarta a zauran majalisar kasar.

Misis Waters ta jam'iyyar left-wing Greens, ta shayar da jaririyarta 'yar wata biyu mai suna Alia Joy, a lokacin da ake kada kuri'a a zauren majalisar ranar Talata.

A shekarar da ta gabata ne, bangaren majalisar wakilai suka marawa majalisar dattijai baya wajen amicewa da barin mata su shayar da jariransu a zauren, sai dai ba a samu wata 'yar majalisa daga ko wanne bangare da ta yi haka ba.

Hakan ya biyo bayan kiraye-kirayen da aka yi a shekarar 2015, lokacin da ministar gwamnati Kelly O'Dwyer ta bukaci da a bai wa masu shayarwa damar don gujewa rashin halattar taron 'yan majalisun.

Misis Water ta ce a shafinta na Facebook, "Muna bukatar karin mata da yawa a majalisar."

"Kuma muna bukatar samun kusanci da iyalanmu da sauki a wuraren ayyukanmu, da kuma rangwamen kula da yara ga kowa," in ji ta.

Sanata Katy Gallagher ta jam'iyyar Labor ta ce, amincewar ya yi dai-dai a wannan lokacin.

Ta shaidawa gidan rediyon kasar cewa," Mata na yin hakan a zauren majalisa a ko ina a fadin duniya."

Ta ce, "Mata za su ci gaba da haihuwa su kuma samu ikon ci gaba da gudanar da ayyukansu a wurin aiki da kuma kula da jariransu a lokaci daya.

Kafin wannan mataki dai, 'yan majalisar wakilai ne kawai suke da izinin zuwa da jariransu zauren majalisa ko wata hukumar gwamnati.

Tun a shekarar 2003 ne, aka bai wa 'yan siyasa damar shayarwa a zauren majalisa.

Sai dai wanna batu ne mai wuyar sha'ani a wasu majalisun dokokin da ke fadin duniya. A shekarar 2016, an soki lamirin wata 'yar majalisar kasar Spaniya, Carolina Bescansa ta jam'iyyar Podemos, kan zuwa da jaririnta zauren majalisar ta shayar da shi.

A shekarar da ta gabata, wani rahoto da aka yi a kan bambancin siyasar Birtaniya, ya bukaci a duba yiwuwar bayar da damar shayarwa a zauren majalisar kasar.

A shekarar 2015 kuwa, wani dan majalisa ya yi gargadin cewa, 'yan jarida za su iya amfani da hakan wajen muzanta mutane.

Labarai masu alaka