Ingantattun hanyoyin yaƙi da talauci guda biyar a Nigeria

EFCC ta kama makudan kudade wadanda ake zargin masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati sun sace Hakkin mallakar hoto EFCC
Image caption Cin hanci na cikin matsalolin da suka fi addabar Najeriya

A daidai lokacin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke cika shekara biyu a kan mulki, manazarta da dama suna ta sharhi kan salon mulkinsa, da nasarorinsa da kuma matsalolin da aka ci karo da su da yadda za a magance su. Muhammad Jameel Yusha'u wani manazarci ne kuma yana aiki da Bankin Raya Kasashen Musulmai wato Islamic Development Bank.

Yaƙi da talauci batu ne da ke ci wa kasashe da dama tuwo a ƙwarya. Wannan shi ya sa da dama daga ƙungiyoyi da cibiyoyin da ke aiki kan raya ƙasa suka mai da hankali wajen yin bincike da gano ingantattun hanyoyin da za a yi amfani da su wajen magance fatara da talauci.

Abin tambaya a nan shi ne, me ake nufi da talauci, ta ƙaƙa za a iya fahimtarsa?

A wani sharhi na musamman da cibiyar ilimi, kimiyya da al'adu ta majalisar dinkin duniya wato (UNESCO) ta wallafa, ta bayyana cewa za a iya fahimtar talauci ne ta fuskoki guda biyu: wato matsanancin talauci, da kuma talauci sese-sese.

Shi matsanancin talauci ana fahimtarsa ne gwargwadon yawan kudaden shigar da mutum ke samu, da wadatar wadannan kudade wajen biyan bukatu na yau da kullum. Wadannan bukatu sun hada da ci da sha da matsuguni da sauransu. A takaice, matsanancin talauci shi ne yanayi na matsi da rashin samun ingantanciyyar rayuwa ta yadda dan Adam zai rayu cikin mutunci ba tare da tagayyara ko tozarta ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Talauci yana gallabar mutane sosai a Afirka

Talauci sese-sese kuwa ana duba shi ne gwargwadon irin kudaden da mutum yake samu idan aka kwatanta da sauran al'umma. Abin da hakan ke nufi shi ne, za a iya samun bambanci tsakanin kasashe bisa yanayinsu da karfin tattalin arzikinsu.

Alal misali, a kasashen Turai mallakar gida, da samun kiwon lafiya, da cin abinci mai kyau, ingancinsa ya kai rayuwar mai tagomashi a wasu yankunan na duniya. Hakazalika idan ka dauki yanayin rayuwa a kasashen Larabawa masu arzikin man fetur, wanda yake matsayin talaka a wasu kasashen zai iya zama mai wadata ne a wasu kasashen.

Daga cikin alkaluman da ake amfani da su wajen gane talauci, shi ne duk mutumin da yake rayuwa da kasa da dalar Amurka biyu, wato kimanin Naira dari bakwai a kudin Nijeriya (bisa canji na kasuwar bayan fage), to wannan mutumin shi ake kira da talaka.

Abin tambaya shi ne: wadanne hanyoyi za a iya amfani da su wajen rage radadin talauci? Wannan makala za ta yi bayani kan guda biyar daga ciki:

Hanya ta daya: Samar da ingantaccen ilimi:

Babbar hanya ta farko wajen magance talauci ita ce samar da ilmi ga jama'a. Domin shi ilmi yana bude kwakwalwar mutum ya fahimci muhimmancin rayuwa cikin alfarma, da kaucewa zaman wulakanci da ci-ma-zaune. Kamar yadda tsohon Shugaban Kasar Tanzaniya Julius Nyerere ya taba bayyanawa, shi ilimi ba wai hanya ce ta kaucewa talauci ba, ilimi makami ne na yakar talauci.

Ko da yake a kasashe masu tasowa ana kallon ilimi a matsayin wani abu ne da sai gwamnati ta gina aji, da samar da malamai sannan za a same shi; tabbas hakan yana da amfani, amma wannan fahimtar takaita hanyar samar da ilimi mai inganci ne.

Wajibin kungiyoyi masu zaman kansu ne, da shugabannin al'umma su duba irin jama'ar da ke cikin wadannan al'umma su tsara hanyoyin ilimantar da jama'a, kan karatu, da rubutu da kuma sana'o'i. Ta haka sai kowanne sashe ya taimaki sashe.

Hanya ta biyu: Koyar da sana'o'i

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bunkasar kasuwanci na rage radadin talauci

Hanya ta biyu wajen yaki da talauci ita ce koyar da sana'o'i kanana da manya. Hakan kuwa ya kamata a fara shi ne tun lokacin yarinta da samar da tsarin ilimi wanda yake nuna muhimmancin sana'a da dogaro da kai, maimakon mayar da hankalin wajen neman aikin albashi.

Wannan na daga cikin hanyoyin da kasar China ta yi amfani da su wajen karfafa tattalin arzikin jama'arta, da tallafa musu wajen inganta fasahar sana'o'i, wanda hakan ya taimaka gaya wajen habaka tattalin arzikin kasar.

Hanya ta uku: Inganta aikin noma

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manoma na kokawa kan rashin tallafi

Muddin ana son magance talauci, to sai an koma ga naduke tsohon ciniki. Bincike da tarihi sun tabbatar da cewa mayar da hankali wajen aikin noma shi ne yake taimakawa kasashe da daidaikun jama'a fita daga kangin talauci.

A wani bincike da hukumar Kungiyar Hadin kan Tattalin Arziki ta kasashen da suka ci gaba wato (OECD) ta wallafa a shekara ta 2010, ta auna yanayin tattalin arzikin kasashe guda 25 domin gano wadanne hanyoyin ne suka fi taimaka musu wajen yaki da talauci.

Sakamakon ya yi amfani da hanyoyi guda uku wajen wannan bincike, wato inganta aikin noma, da hanyoyin samar da ci gaba amma ba na aikin noma ba, sai kuma kudaden da 'yan kasashen waje suke aikawa da su zuwa kasashensu na asali.

Binciken ya tabbatar da cewa kashi 12 cikin 25 sun rage radadin talauci a kasashensu ta hanyar noma. Don haka duk mai son yin sallama da talauci, ya dauki fatanya ya nufi gona.

Hanya ta hudu: Bayar da bashi da tallafi ga masu son yin sana'a

Hanya ta hudu ta magance talauci ita ce samar da ba shi musamman mara sharadi ko kudin ruwa ga masu son zuba jari kan karamar sana'a. Hakan za a iya yi ne ta bangaren gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da kuma tsarin adashi tsakanin jama'a.

Misali na kusa shi ne shirin Babban Bankin Najeriya (CBN) na tallafawa manoma da kudade domin inganta aikin noma. Kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, daga cikin wadanda za su fi zuwa aikin Hajji a bana a wasu jihohin Najeriya, akwai manoma wadanda suka ci gajiyar irin wannan shiri.

Amma bai kamata jama'a su ce sai sun jira gwamnati ba. Mazauna unguwanni za su iya yin adashin gata tsakaninsu, sannan duk wanda ya dauka, maimakon ya yi watanda da kudin sai ya zuba jari a wata sana'a.

Hanya ta biyar: Yin amfani da hanyoyin zamani na kimiyya da fasaha

Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption 'Amfani da kafofin sadarwa na zamani wajen tallata kaya na da fa'ida'

A wannan karnin, hanyoyin fasaha na zamani suna saukake yadda yanayin rayuwa yake. Don haka koyawa jama'a yadda ake amfani da wadannan hanyoyi zai taimaka su yi amfani da basirar da Allah Ya yi musu wajen tallata sana'a ko koyar da ita.

Misali, kusan matasa a yanzu da dama suna da shafin sada zumunta na Facebook, ko Twitter, ko Instagram da sauransu.

Maimakon yin amfani da wadannan shafuka domin yin hira, za a iya sauya su wajen tallan sana'oi da kuma koyar da dabarun yaki da talauci.

Bugu da kari, za a iya yin amfani da su wajen neman jari. Akwai tsari na neman tallafi ta duniyar gizo wato Crowdfunding, duk wadannan dabaru ne na samun jari a zamanance domin kaucewa rayuwar kunci.

Kamar yadda Hausawa ke cewa, dabara ta ragewa mai shiga rijiya.

Dokta Muhammad Jameel Yusha'u, tsohon ma'aikacin BBC ne.