Shin ciwo ne ko jaraba ke sa ƙaruwar fyaɗe ga yara?

'yan sanda sun ce matsalar na karuwa a Kano
Image caption 'Yan sanda sun ce matsalar na karuwa a Kano

Fyaɗe, babbar matsala ce da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, lamarin da ke ci wa iyaye da hukumomi tuwo a ƙwarya.

Daga Ikko zuwa Kano, Abia zuwa Damaturu, Uyo zuwa Birnin Kebbi, ko wa ka tambaya zai gaya maka cewa wannan matsala na neman ta gagari kundila.

Wani rahoto da ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta fitar a shekarar 2014, ya bayyana yadda jami'an 'yan sanda ke yi wa matan da suka kama fyade "da sauran cin zarafi a bainar jama'a".

Rahoton ya ce akan yi hakan ne lokacin da aka kai matan caji ofis, ko kuma a lokacin da matan suka ziyarci mazan da ake tsare da su a ofisoshin 'yan sandan ƙasar.

'Yan sandan dai sun sha musunta irin wadannan zarge-zarge a baya.

Wannan lamari bai taƙaita ga jami'an tsaro ba, domin kuwa akwai rahotanni da dama daga yankuna daban-daban na ƙasar da ke nuna yadda ko dai mahaifi ke yi wa 'yarsa ta cikinsa fyaɗe, ko ɗan shekara 70 da ke yi wa 'yar shekara bakwai fyaɗe ko kuma yadda samari kan yi wa 'yan mata fyaɗe.

Wani abu mafi tayar da hankali game da wannan matsala shi ne yadda ake samun masu yi wa 'yan ƙananan yara, ciki har da jarirai, fyaɗe kamar yadda ta faru cikin birnin Kano a kwanakin baya, inda ake zargin wani mutum ya yi wa wata jaririya 'yar wata takwas fyaɗe.

'Mutum 547 aka yi wa fyade a 2016'

Lamarin dai kan bai wa mutane mamaki, musammam idan an yi la'akari da cewa jaririya 'yar watanni kaɗan a duniya, ba ta ma san abin da rayuwa ke ciki ba ballantana a ce za ta fahimci abin da aka yi mata.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Magaji Musa Majiya ya shaida min cewa fyaɗe babbar matsala ce da babu kamarta a jihar.

A cewarsa, "A shekarar 2016 mun samu rahotannin fyaɗe 547 daga birnin da ƙauyukan Kano. Mun kai dukkansu gaban ƙuliya kuma an ɗaure 10 daga cikinsu, kama daga shekara biyar zuwa 14".

DSP Majiya ya ƙara da cewa wannan matsala ta yawaita a jihar "kuma kashi 95 cikin 100 na mutanen da ake yi wa fyaɗe yara ne 'yan ƙasa da shekara goma."

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kashi 95 cikin 100 na fyaden da ake yi a Kano ya shafi kananan yara

"Akasarin mutanen da ake kamawa kan zargin sun yi wa ƙananan yara fyade sukan ce tsautsayi ne ko sharrin shaiɗan, ko da yake abin da muke ji daga jama'ar gari shi ne: Ana yi musu ne domin yin tsafe-tsafe.

Ya ce a ganinsa matsalar na ƙaruwa ne saboda yanzu mutane suna fitowa fili suna fadar abin da ya faru sabanin a baya inda suke ɓoyewa domin gudun tsangwama."

Magaji Musa Majiya ya ƙara da cewa rundunar 'yan sanda ta haɗa gwiwa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da 'yan Hisbah don ganin an samu raguwar fyaɗe, yana mai cewa "muna kuma tuntuɓar Malamai da Limaman Coci-Coci domin su taka rawa wajen kawo ƙarshen wannan matsala."

Ɗaya daga cikin masu fafutukar kare haƙƙin mata, Malama Nana Gwadabe ta shaida min cewa rashin zartar da tsattsauran hukunci a kan mutanen da aka samu da hannu a fyaɗe ne ke ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da yin abin da suke yi.

A cewarta "Idan ka dubi lamarin za ka ga cewa ba a yin hukunci mai tsauri kan masu aikata wannan ta'asa."

'Tsananin bukatar yin jima'i na taka rawa'

Ta ƙara da cewa hakan ne ya sa suke bibiyar shari'ar da ake yi wa mutumin da ake zargi da yi wa jaririya 'yar wata takwas fyaɗe domin ganin an yi adalci; amma "muna kira ga 'yan majalisa su yi doka da za ta tanadi tsattsauran hukunci a kan irinsa".

Likitoci dai sun ce wannan matsala na faruwa ne sakamakon ciwon ƙwaƙwalwar da ke damun mutanen da ke aikata fyaɗe.

Dr Attahiru Muhammad Bello, wani likitan ƙwaƙwalwa ne a hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar Adamawa, kuma ya faɗa min cewa matsalar gagaruma ce.

"Yawancin masu yi wa ƙananan yara fyade suna fama da cutar da a Turance ake kira paraphilia, wato jarabar bukatar yin jima'i, ko da kuwa da wani abu kamar ƙarfe ne ko kuma ƙananan yara."

Ya ce a kasashen da aka ci gaba ana sanya musu ido idan aka ga suna nuna irin wannan ɗabi'u tun suna yara ta yadda za a rika yi musu magani da ba su shawarwari.

'Tsattsauran hukunci'

Sai dai Malaman addini na ganin ana samun yawaitar fyaɗe musammam a kan kananan yara ne saboda neman abin duniya.

Dr Abdullahi Pakistan, wani Malamin addinin musulunci a birnin Kano ya ce abu uku ne ke haddasa wannan matsala:

"Tsananin neman duniya, inda za ka ga boka ko matsafi ya bukaci mutum ya aikata fyade ko ya cire agarar wani, ko kuma ya tono gawa domin biyan bukatunsa.

Sai kuma shaye-shaye da ke batar da hanakalin mutane ta yadda ba sa sanin abin da suke aikatawa, da kuma tasowa cikin rashin tarbiyya.

Mutane ba su san abin da ake kira tausayi ba. Duk mutumin da bai samu tausayi ba, ba zai tausayawa wani ba," a cewar babban malamin Islamar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Hisbah da 'yan sanda na jajircewa wajen kawo karshen fyade a Kano

Malamin ya ƙara da cewa ya kamata hukumomi su rika yanke tsattsauran hukuncin kan duk mutumin da aka samu da laifin fyaɗe, sannan a gefe ɗaya kuma iyaye su duƙufa wajen yi wa 'ya'yansu tarbiyya baya ga wa'azi da Malamai za su mayar da hankali wajen yi wa al'umma kan illar wannan matsala.

Da alama dai wannan batu zai ci gaba da jan hankalin mutane a Najeriya, kuma zai ci gaba da kasancewa babban ƙalubale ga 'yan ƙasar da ma hukumomi, wadanda ake buƙatar su ɗauki matakai ƙwarara domin shawo kansa.