Kotu ta hana Andrew Yakubu miliyoyin daloli

Yakubu

Wata babbar kotu a Kano ta ki amincewa da bukatar da ya tsohon manajan kamfanin mai na Najeriya NNPC, Andrew Yakubu ya shigar, inda ya nemi da a watsar da umarnin da kotun ta bai wa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati cewa ta damkawa gwamnatin tarayya kudin.

A watan Fabrairu ne kotu ta bai wa hukumar EFCC damar mallakawa gwamnati sama da dala miliyan 9.8 da aka samu daga gidan Mista Yakubu a Kaduna.

Mai shari'a Zainab Abubakar ce ta yanke hukunci kan bukatar wadda lauyan Mista Yakubu ya shigar, inda ta ce kotu tana da hurumin sauraron karar ba kamar yadda lauyan ya nuna cewa hakan ba daidai ba ne.

Wakilin BBC a Kano ya ce mai shari'ar ta kuma ce bukatar Mista Yakubu da ke neman a yi watsi da shari'ar ba ta da wata madogara a shari'ance, kuma dokar kasa ta bai wa EFCC damar neman umarnin a mika kudin ga gwamnati.

Tuni EFCC ta fara tuhumar tsohon shugaban NNPC din a kan kudaden da aka samu a gidan nasa.

Labarai masu alaka