'Yan matan Chibok: Ya rayuwarsu za ta kasance?

'Yan matan Chibok
Image caption An sace 'yan matan Chibok din a matsayin yara mata, amma a yanzu an sako su a matsayin mata matasa.

Amma kamar yadda wakilin BBC, Alastair Leithead yake bincike, ba lallai bane su iya komawa gida.

Ba sako 'yan matan ne zai kawo karshen tashin hankali da ke tattare da sace su da kungiyar Boko Haram tayi ba.

A zahiri ma, wannan ne somawar wata gwagwarmayar komawa suyi rayuwa cikin danginsu da al'ummarsu.

An sace 'yan matan Chibok din a matsayin yara mata, amma a yanzu an sako su a matsayin mata matasa.

Yanzu sun tashi daga 'yan mata sun koma manyan mata sakamakon kama su da aka yi.

'Yan matan 82, wadanda aka sako, za su gana na dan lokaci da danginsu a cikin 'yan kwanakin nan masu zuwa.

Wani wanda ke wakiltar kungiyar iyayen Chibok ya kai musu ziyara, domin ya gano wadanda suka dawo a jerin sunayen 'yan matan da yake da su a rubuce kuma ya tabbatar wa wadanda ke jira labari mai dadi ko kuma akasin haka.

Wadanda aka gayyata su zo, za su ji tafiyar zata kasance tamkar tafiya mafi nisa da suka taba yi.

An sake garkuwa dasu?

Image caption Wasu iyalan 'yan matan so su ke yi kawai 'yan matansu su dawo gida

Idan iyayen da 'yan matan suka hadu za su yi kukan murna ganin cewa dole akwai sauye sauye a cikin shekaru uku da suka gabata.

Daga nan sai me?

Idan dai har za a yi amfani da matakin da aka dauka a lokacin da aka sako 'yan mata 21 a cikin oktoban da ya gabata, da kuma kadan daga ciki da suka tsere, to suma 82 din da aka sako za a bi wannan matakin domin inganta rayuwarsu.

Wannan zai kasance suna karkashin kulawar gwamnati ne, ko kuma gwamnati na garkuwa da su ne ya dai danganta da yadda kake kallon lamarin.

Wasu iyalan na goyon bayan matakin, wasu kuma na fushin cewa bayan wata shida da sako yaran daga hannun kungiyar Boko Haram, har yanzu yaransu basu dawo garesu ba.

Daya daga cikin iyayen wadanda suka ziyarci wani ginin gwamnati a Abuja babban birnin kasar, a makon da ya gabata, sun ce ana kula da yaran yadda ya kamata kuma suna zama cikin kwanciyar hankali.

Hakkin mallakar hoto OFFICE OF THE FIRST LADY
Image caption Ana koya musu ayyukan hannu kamar dinki da saka kuma ana koya musu karatu

Ali Maiyanga Askira wanda ya ziyarci 'yarshi Maryam ya ce "Naji dadin halin da naga matan a ciki, kalau suke."

"Fata na ace tana tare damu, amma ba zan iya bata kulawar da gwamnati take bata ba."

"Ana koya musu ayyukan hannu kamar dinki da saka, kuma ana koya musu karatu."

Ministan ilimi ya shaida mana cewa cikin watanni hudu za su koma makaranta.

"Na gamsu da duk wata shawara da gwamnati ta yanke."

Amma wasu iyalan kawai so su ke yi 'yan matansu su koma gare su.

An fuskanci fushi a lokacin kirismeti da aka kawo su Chibok su gana da 'yan uwansu, amma ba a bar su sun je gida ba.

An kai su gidan wani dan siyasa kuma an bar su sun gana da 'yan unwasu na dan lokaci ne kawai.

"Na kasa yadda cewa 'yata ta zo kusa da gida, amma kuma ba za ta iya zuwa gida ba." a cewar wani mahaifi.

Amma shugaban al'ummar Chibok dake Abuja, Tsambido Hosea, ya ce an gayyaci iyaye su zo Abuja domin su gana dasu.

Image caption Wasu daga cikin 'yan matan da aka sace Musulmai sun zama kiristoci

"Suna cibiyar saisaita tunaninsu. Gwamnati ta ce tana ba su umarnin yadda za su koma makaranta, a cewar shi.

Ko za a bar su suje gida, ko akasin haka, al'ummar bata damu da cewar suna karkashin kulawar gwamnati ba.

"Mun san cewa suna hannun wadanda muka sani, ba sabanin haka ba, kuma za mu iya kiransu kuma su amsa a duk lokacin da suka ga dama."

"Ya bambanta da lokacin da suke hannu kungiyar 'yan ta'adda."

Masu nazari kan halayyar dan Adam wadanda suka yi aiki tare da 'yan matan da aka fara sakowa, sun ce gara a ce suna tare da 'yan unwansu, domin za su fi sakewa a al'umma.

Ana kuma zargin cewa ba a bari 'yan matan da aka sako da farko sun je gida ba saboda an yayata dawowarsu kuma hakan zai iya jawo a kara sace su.

Akwai lokutan da aka bari wasu wadanda ba 'yan matan Chibok suka koma gida ba tare da an basu horo da zai canza halayyansu ba, kuma haka yasa aka rika ware su a al'umma ko ma wani bangare na 'yan uwansu.

Wasu Musulmai sun zama kiristoci kuma wasu sun auri 'yan kungiyar boko Haram kuma sun hayayyafa da su wanda ya jawo ake kyamatarsu.

Tabbas da zarar an kawo karshen ta'addancin, tasirin barnar 'yan ta'addan zai dade, sai dai nan da nan za su iya komawa su ci gaba da rayuwarsu tare da al'ummarsu.

Labarai masu alaka