Nigeria: 'A fitar da rahoton binciken Babachir'

Farfesa Yemi Osinbajo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Farfesa Yemi Osinbajo

A Najeriya, wasu masu fafutukar yaki da cin hanci a kasar sun bukaci mukaddashin shugaban kasa daya gaggauta fitar da rahoton daya bincike Babachir David Lawal, Sakataren gwamnatin da aka dakatar bisa zargin aikata almundahana.

Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al'umma ta CITAD da ke arewa maso gabashin Najeriya na daya daga cikin kungiyoyin da suka fara irin wannan kiraye kiraye.

Shugaban cibiyar Comrade Kabiru Sa'idu Dakata ya ce 'yan Najeriya sun zura ido suga an fitar da sakamakon binciken inda ya ce Jama'a da dama musamman masu fafutukar yaki da cin hanci a kasar na ganin beken gwamnatin saboda kin mika rahoton.

A cewar su, rashin gabatar da rahoton ka iya sanya shakku a zukatan al'umma game da yaki da cin hanci da rashawa na gwamnatin kasar.

Tun da farko dai an tsara cewa kwamitin zai mika rahoton sa ne ranar 3 Mayu amma kuma aka dage zuwa ranar Litini 8 ga watan Mayu wanda kuma ba'a gabatar ba.

Kwamitin binciken da shugaba Muhammadu Buhari ya kafa dai ya hada da Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro, Majo Janar Babagana Monguno mai ritaya da kuma babban lauyan Najeriya, Abubakar Malami.