Katanga ta kashe 'yan biki 22 a India

Indiya katanga Hakkin mallakar hoto Banwari Upadhyay
Image caption Katangar ta fadi ne bayan da aka yi tsawa

'Yan sanda a Indiya sun ce a kalla mutum 22 sun mutu, wadanda yawancin su yara ne, sakamakon faduwar wata katanga ana tsakiyar shagalin biki a yammacin birnin Jaipur.

Mutum 26 kuma sun samu raunuka, wadanda 15 daga cikin su raunin nasu mai tsanani ne.

An hanzarta kai marasa lafiyar asibiti da ke kusa da inda lamarin ya faru don a duba lafiyarsu.

Wani dan sanda Anil Tank ya shaida wa manema labarai cewa bakin da suka halarci bikin na tsakiyar rakashewa sai kawai ruwan sama ya sauka, daga bisani kuma sai aka yi wata tsawa mai karfin gaske.

To daga nan ne sai mutanen suka nemi wajen fakewa, a nan ne wani bangare na katangar wajen da suke ta zube ta kuma fadi kan mutane da dama.

Rahotanni sun ce an jera abincin bikin a kusa da katangar ne.

Mista Tank ya ce tsawon katangar ya kai mita 27 yayin da fadinta kuma ya kai inci 12 zuwa 13.

Gundumar Bharatpur na da nisan kilomita 200 daga Kudancin babban birnin kasar Delhi.

Labarai masu alaka