Nigeria: Majalisa ta amince da kasafin kudin 2017

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya ce kasafin kudin zai taimaka wurin farfado da tattalin arzikin kasar

Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kasafin kudin kasar na 2017 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata a watan Disambar da ya gabata.

Kasafin ya nuna cewa kasar za ta kashe naira tiriliyan 7.44 kwatankwacin dala biliyan 24.43.

A karon farko majalisar ta kuma fayyace adadin kason da aka ware mata, wanda ya kai naira biliyan 125, sakamakon matsin lamba daga kungiyoyin masu fafutika.

Batun abin da majalisar ke kashe wa dai ya dade yana jawo ce-ce-kuce a kasar, inda wasu ke zargin suna dibar makudan kudade, lamarin da suka sha musanta wa.

A yanzu za a mika kasafin ga shugaban kasa domin sa hannu kafin ya zama doka.

An tsara kasafin kudin ne a kan hasashen cewa Najeriya za ta rinka samar da ganga miliyan 2.2 ta danyan mai a duk rana, inda za a sayar da shi a kan dala 52 kan kowacce ganga.

Kuma za a yi musayar kudin kasar a kan naira 305 kan kowacce dala daya.

'Yan majalisar sun shafe wata biyar kafin su amince da kasafin, abin da wasu ke ganin zai iya yin illa ga tattalin arzikin kasar.

A bara ne tattalin arzikin kasar ya samu tawa ya a karon farko cikin shekara 20.

Najeriya kasa ce da ta dogara da man fetur wajen samun mafi yawan kudaden shigarta, sai dai faduwar farashin a kasuwannin duniya ya yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikinta.

Labarai masu alaka