''Yan matan Chibok za su koma makaranta a watan Satumba'

Hajiya Aisha Jummai Al'assan
Image caption Ministar harkokin mata A'isha Alhassan ta ce gwamnati za ta ci gaba da neman shawarar kwararru game da tunanin yaran

Gwamnatin Najeriya ta ce 'yan matan Chibok 103 da kungiyar Boko Haram ta sako bayan sun shafe shekara uku a hannunta za su koma makaranta a watan Satumba.

Ministar harkokin mata ta kasar Hajiya Aisha Jummai Alhassan, ta ce zuwa wannan lokaci 'yan matan za su samu nutsuwa don komawa karatunsu.

Ta ce za a rufe cibiyar bayar da kula ga yaran da ke Abuja, inda aka ajiye wasu daga cikin 'yan matan da zarar sun koma makaranta.

Hajiya Jummai ta ce 'yan matan dai sun hada da 83 da aka sako ranar Asabar din da ta gabata.

Ta shaida wa manema labarai cewa 'yan matan na cikin hayyacinsu da farin ciki in an kwatanta da yadda aka sako 'yan mata 21 a shekarar da ta gabata.

Ta kara da cewa, "suna cikin hankalinsu da hayyacinsu fiye da 21 na farkon da aka fara sakowa, kuma na yi amanna cewa tsakanin zuwa watan Satumba wadannan da aka sako yanzu za su samu damar sakin jikinsu, kuma hakan zai ba mu damar daukarsu zuwa makaranta a watan Satumba," in ji Ministar.

Ta kara da cewa, "A dan karamin ilimina, ba na likita ba, Ina jin cewa suna cikin koshin lafiya."

Ministar ta kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da neman shawarar kwararru game da tunanin yaran.

Ta ce za a rufe cibiyar koyon sana'ar, wadda nan ce aka mayar cibiyar sauya tunani da yaran ke ciki, da zarar yaran sun koma karatu.

Hajiya Jummai ta ce 'yan matan na samun kula da ta fuskar sauya tunaninsu a cibiyar, kuma basu da wata "damuwa".

Su ma 'yan matan da aka ceto ranar Asabar din za a kai su cibiyar koyon sana'a, inda za su samu kwarewa.

Ta musanta rahotonnin da ke cewa an hana 'yan matan ganin iyayensu ta kuma ce ba a hana su barin cibiyar ba.

Ta ce yanzu haka wata na ziyarar iyayenta, sai dai kuma an boye sirrinta.

Yanzu haka dai kungiyar ta Boko Haram na rike da kusan 'yan mata 100 daga cikin kusan 276 da ta sace daga makaranta Chibok shekara uku da ta gabata.

Haka kuma kungiyar ta sace tare da yin garkuwa da dubban mutane da ke yankin lokacin rikicin.

An dai yi amanna cewa wasu daga cikin 'yan matan sun auri 'yan kungiyar kuma har sun haihu tare da su.

Hajiya Aisha ta kuma ce suna aiki tare da iyaye don tantance yaran 83 da aka sako ranar Asabar.

Labarai masu alaka