Faɗa tsakanin giwaye da mutane na ƙamari a Sri Lanka

Raja Thurai
Image caption Raja Thurai na dawowa daga kogi

Faɗa tsakanin mutane da giwaye na daɗa ƙamari a ƙasar Sri Lanka fiye da ko ina a fadin duniya, inda mutane 70 da giwaye fiye 250 ke mutuwa a ko wacce shekara.

Ana samun irin wannan fada tsakanin mutane da giwaye, a yankunan da ba mazauna, tsawon lokaci sakamakon yakin da ake yi a kasar.

A watan Yuni da ya gabata, a lokacin da Raja Thurai da 'yarsa Sulojini mai shekara shida ke dawowa daga kogi da yamma, sai ga wata giwa daga cikin daji, nan da nan ta kai musu hari.

Mista Thurai ya ce, ''Giwar ta daga ni sama da jefar da ni gefe. Na suma, kafin in farfado, sai na ga 'yata a kusa da ni tuni har ta mutu.

Hakan ya faru ne kusa da kauyen Mista Thurai da ke gabashin lardin Paavatkodichchinai a Sri Lanka.

Ya ce, ''Na rasa yarana biyu- na rasa ɗana a lokacin yaki ita kuma Sulojini giwa ce ta kashe ta.

Kabilar Tamil wadanda su ne marasa rinjaye a Sri Lanka ne ke zama a lardin Paavatkodichchinai, kamar al'umomin da ke gabashin tsibirin.

A lokacin yakin, saboda 'yan tawayen Tamil Tiger da ke gabashin lardin ya sa dakarun gwamnati suka mai da hankali a kan lardi a lokacin da yakin ya yi tsanani.

Mutanen da sun fi son cin kan giwaye?

Abin da ba ka sani ba game da giwaye

Ka san kimiyyar da ke tattare da kashin kare da mutum da giwa?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yanzu giwaye suna shigowa cikin gari domin neman abinci

Raja Thurai da iyalinsa sun zauna a sansanin 'yan gudun hijira a shekarar 2007.

Da suka dawo bayan yakin an gama yakin a shekarar 2009, giwaye sun kutsa musu a yankin.

A yanzu giwayen na ci gaba da zamewa mutanen yanki abin fargaba, musamman da daddare a lokacin da suke shigowa kauyen don neman abinci.

Mista Thurai ya ce, "Muna korarsu amma sai su dinga dawowa. Ko wacce rana ba ma yin bacci isasshe, ko jiya ma haka."

Gidansa na daya daga cikin wadanda ke fuskantar irin wannan hari da giwayen ke kai wa da daddare. A gaban gidan akwai bishiyoyin mangoro manya guda biyu, har yanzu akwai bangaren da bangon ya rushe - wanda giwa ce ta rusa shi a wani dare da ta kai hari, tun kafin 'yarsu Sulojini ta mutu.

Indrani, matar Raja Thurai ta ce, ''Hakan ya faru ne da misalin karfe 2 na tsakar dare. Giwar ta samu nasarar shigowa cikin gidan, inda ta rusa bango da rufin kwanon gidan."

Image caption Indrani na rike da silifa din 'yarta Sulojini da giwa ta kashe, wanda shi kadai ne abin da suke tuna ta da shi

Ta kara da cewa Sulojini ta ji tsoro har sai da ta yi zazzabi.

Basu da hoton 'yarsu da suka rasa amma suna da silifas din da ke kafarta a lokacin da giwa ta kashe ta.

Tun wannan lokaci, 'yan ƙauyen sun shirya nasu tsaron a unguwar. Kowa na da abin tayar da tartsatsin wuta domin korar giwayen, amma masana na cewa ba hakan ne zai magance matsalar ba.

Wani jami'in gandun daji Dr Pruthu Fernando ya dade yana amfani da kwarewarsa wajen ganin ya kawo mafita ga yawan fadan da ake samu tsakanin mutane da giwaye a Sri Lanka, ya ce, "Mutane suna yin shiri tamkar masu zuwa yaki."

''Idan giwar ta zo tana neman abinci, sai mutane su yi mata tsawa. Sai ka ga giwar ta ji tsoro, ta gudu. Daga baya sai giwar ta lura cewa mutane ihu kawai suke yi, ba zasu iya cutar da ita ba. Don haka daga baya ko da mutane sun mata tsawar ba ta komawa sai ta je ta aikata abin da ya kawo ta."

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yara na wasa kusa da wata giwa wani rafin a Kataragama a gabashin Sri Lanka

'Yan kauyen sun yi amfani da hanyoyi daban-daban don korar giwayen: da farko suna jifan giwayen da duwatsu, sai kuma suka fara korar su da itacen wuta. A karshe dai shi ne suka fara amfani da tartsatsin wuta da ake jefawa sama.

Fernando ya ce, "Wasu sai su tashi kamar bam, amma ba a dade ba sai giwayen suka gane cewa kara ce kawai, don haka suka ci gaba da kai hari. A karshe dai sai mutane suka fara harbin giwayen. Duk wadannan abubuwa fito-na-fito ne."

Fernando ya bayar da shawarar amfanin da shingen lantarki, a wasu muhimman lokuta a shekara.

Giwayen na iya yawo a gonaki a lokacin da ba a yi shuka ba, sai dai manoma su kan gina shinge idan suka fara shuka.

Ya kara da cewa, "Manoman na cire shingen bayan sun yi girbi."

Tuni dai Sri Lanka na da shingayen wutar lantarki da dama amma yawancinsu ba a sanya su a inda ya dace ba.

Mista Fernando ya ce, "A da ana amfani da su ne don killace kadarori ko gandun dazuzzuka. Amma daga baya giwaye suka lalata su. da akwai da iyaka tsakanin gidaje da kogi. Ana bukatar yin shingayen kusa da inda mutane ke gudanar da al'amuransu don a nan aka fi bukatar su."

Wasu 'yan Sri Lankan na rayuwar zaman lafiya da giwaye masu fada .

Al'ummar Rathugala Veddha da ke kusa da kogin Gal Oya a kudu maso gabashin Sri Lanka - wadanda kakanin kakanninsu ne ainihin mazauna tsibirin, suna addu'a domin neman kariya a duk lokacin da suka shiga daji. Ba wanda ke iya tunawa ranar da wani ya ji rauni ballantana a ce giwa ta kashe mutum.

Poramal Aththo ya ce, ''Muna ji a cikin jikinmu idan giwaye na kusa. Muna da wannan baiwar.''

Image caption Wannan al'ummar sun yarda suna da baiwar da giwaye ba za su iya kashe su ba

'Yan kauyen na iya sanin giwaye na kusa soboda suna rayuwa tare dasu tsawon lokaci.

Poramal Aththo ya ce, "Zan iya koyawa wasu yan Sri Lankan yadda za su kare kansu amma ba abin da za'a iya koya a rana daya ba ne.

A babgaren giwayen, wata 'yar giwa da aka bai wa suna Leila, an ceto ta ne bayan da ta ci hukka patta, wani bam na gargajiya, da ta yi tsammanin abinci ne. Ya tashi a cikinta, inda ya lalata bakinta da harshenta.

Ana kula da Leila a Hukumar kula da dabobin daji kusa da birnin Polonnaruwa.

Dr Pinidiyage Manoj Akalanka ya ce, mutuwar giwaye sakamakon cin hukka pattas na karuwa. Yawancinsu na mutuwa. Idan ba su iya cin abinci ba sai yunwa ta kashesu.

A wannan gundumar ana samun irin hakan kusa 40 a ko wacce shekara.

Image caption 'Yar giwa Leila ta ci bam a matsayin abinci

Amma Leila ta koyy yadda za ta ci abinci shi ya sa nan ba da dadewa ba za a mayar da ita cikin daji.

Bayan da Sulojini ta mutu a Paavatkodichchinai, aka dawo da wutar lankarki a kauyen.

Gwamnati ta kan bai wa iyalan da giwaye suka kashe musu 'yan uwa dala 3,278.

Amma ga iyayen 'yar yarinya Sulojin, babu wani adadi da za a ba su ya sa su manta da radadin mutuwar 'yarsu, wacce ba ta mutu a hanyar dawowa daga wankan da ta je rafi, sai dan silifas dinta da suke tuna ta da shi.

Labarai masu alaka