Nigeria: PDP ta yiwa Bola Tinubu raddi

Bola Tinubu na cikin jiga jigan jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bola Tinubu na cikin jiga jigan jam'iyyar APC mai mulki a Nigeria

Wasu manyan 'yan siyasa na bangaren adawa a Najeriya sun fara mayar da martani kan kalaman da jagoran jamiyyar APC mai mulkin Sanata Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Rahotanni sun ambato Sanata Tinubu yana cewa babu wata jam'iyyar adawa da za ta lashe ko kujera daya a zaben kananan hukumomi da za a yi a jihar Legas nan gaba kadan.

Sai dai wasu 'yan adawa a jihar sun ce mafarki kawai jagoran na APC ke yi.

A cewar Hon Muhammad Mairiga wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar, 'tun ba yau ba jam'iyyar PDP ke kayar da Bola Tinubu a zabubbukan da aka gudanar mazabun sa'.

Hukumar zabe ta jihar Legas dai ta shirya gudanar da zaben kananan hukumomi ne a watan Yulin 2017.