Nigeria: Mutum miliyan 57 na fama da matsalar ruwan sha

Miliyoyin mutane a Najeriya na fama da matsalar ruwan sha Hakkin mallakar hoto TOMMY TRENCHARD / IFRC
Image caption Miliyoyin mutane a Najeriya na fama da matsalar ruwan sha

A Najeriya, kungiyar bayar da tallafin nan ta Amurka USAID, ta kaddamar da wani sabon tallafi na dala miliyan biyu da rabi, domin samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma tsaftar muhalli a jihohin Kaduna da Bauchi.

Za'a kwashe shekaru biyu ana wannan shiri a jihohin, wadanda a 'yan kwanakin nan suka sami tallafi mai tsoka domin gyara harkar samar da ruwan sha da tsafta da kuma kula da lafiyar al'ummar da ke zaune a Jihohin.

Kungiyar ta USAID, na aiki ne tare da ma'aikatun samar da ruwa a jihohin biyu domin inganta ayyukan samar da ruwan sha.

Majalisar dinkin duniya ta kiyasta cewa, kimanin mutane miliyan 57 ke fuskantar matsalar samun tsaftataccen ruwan sha a Najeriya.

Kazalika majalisar ta ce, yara kusan miliyan guda na mutuwa a duk shekara sakamakon shan gurbataccen ruwa.

Al'ummar jihohin da zasu amfana da wannan tallafi, sun yi kira ga gwamnatocinsu da suyi musu abinda ya dace kudin tallafin, ta yadda za a inganta rayuwar miliyoyin jama'a.

Labarai masu alaka