Nigeria: Mutum 50 sun mutu a hatsarin mota a Kebbi

Najeriya hatsari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana yawan samun afkuwar hadurra a titunan Najeriya

Rahotanni daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa, fiye da mutum 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hatsarin mota a ranar Alhamis da yamma.

Wani Likita da 'mummunan lamarin' ya faru a kan idonsa kusa da kauyen Tsamiya, ya shaida wa BBC cewa, wasu mutanen fiye da 40 kuma sun jikkata.

Likitan ya ce lamarin ya faru ne yayin da babbar motar tirela da matafiyan ke ciki ta kifa.

Wadanda abin ya rutsa da su 'yan kasuwa ne wadanda suke dawowa daga wata babbar kasuwar kayan abinci da dabbobi da ke kan iyakar kasar Nijar da Jamhuriyyar Benin.

Har zuwa yanzu jami'an kare afkuwar hadura na jihar Kebbin ba su tabbatar da iya adadin wadanda suka mutun ba, amma sun ce sun haura mutum 50.

Afkuwar hadurra a kan titunan Najeriya wani abu ne da yake yawan faruwa, duk da irin kokarin da hukumar kare afkuwar hadurra ke cewa na yi don rage samun hakan.

Sai dai masu sharhi da dama na ganin ana yawan samun hadurran ne saboda rashin kyan titunan kasar, da yadda masu motoci ke sharara gudu, da yin lodin da ya fi karfin motocin da kuma amfani da motocin da watakila sun gama gajiya don an shafe shekaru da dama ana amfani da su ba tare da ana duba lafiyarsu da kyau ba.