Hotunan al'amuran da suka faru a Afirka a wannan makon

Wasu zaɓaɓɓun hotuna abubuwan da suka faru a sassan Afirka a makon nan.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Asabar ne, aka dauki hoton wannan mutumim yana busa sarewa a lokacin da ake gudanar da bikin farauta na Aboakyer, wanda yake nuna cewa an kama gada da hannu ba tare da wani makami ba a garin Winneba da ke kasar Ghana.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A lokacin bikin kungiyoyin mafarauta biyu sun gudanar da gasar kama gada da hannunsu, ko da sanda, ko kulki, sannan a kawo ta gaban shugaba.
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Sarkin Winneba Neenyi Garthey na zagayawa sau uku a kan gadar da aka kama kafin a bayyana wanda ya lashe gasar.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A wannan ranar ne kuma masu zanga-zanga suka yi wani gangami na nuna bukatarsu kan halatta amfani da tabar wiwi a birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mai zanga-zanga na nuna goyon bayansa a kan halatta shan wiwi ta hanyar busa hayaki sama.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan gudun hijira na kallon tsibirin Gozo na kasar Malta bayan da aka gudanar da aikin ceton 'yan ci-rani a gabar tekun kasar Libya.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dubban 'yan ci-rani na ci gaba da nausawa kogin Bahar Rum don yin tafiya mai cike da hadari zuwa kasashen Turai.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Lahadi ne, aka sako wasu 'yan matan chibok 82 , inda suka yi layi don ganawa da shugaban kasar Najeriya a fadarsa da ke babban birnin kasar, Abuja.

Labarai masu alaka