Ana tuhumar gimbiyoyi saboda bautar da masu yi musu hidima

Masu karar sun ce, an hana su barin otel din kuma ana tilasta musu cin ragowar abincin gimbiyoyin.
Image caption Masu karar sun ce, an hana su barin otel din kuma ana tilasta musu cin ragowar abincin gimbiyoyin.

Gimbiyoyi takwas a garin Brussels na fuskantar shari'a akan fatauci da kuma cin zarafin bayi a lokacin da suke zaune tare da su.

A shekarar 2008 ne Sheikha Hamda al-Nahyan da 'ya'yanta bakwai suka karbi hayar wasu dakuna na sama da watanni takwas a wani katafaren otel.

Sun tafi da masu yi masu hidima fiye da 20, wadanda suka dauko daga hadaddiyar daular Larabawa, kuma ana zargin sun rike su a wani hali mai kama da bauta.

Masu karar sun ce, an hana su barin otel din kuma ana tilasta musu cin ragowar abincin gimbiyoyin.

Idan aka same su da laifi, za su fuskanci hukuncin tarar dubban daruruwan Euro, har da zaman kurkuku, sai dai masu fafutukar kare hakkin dan adam sun ce abu ne mai matukar wahala Hadaddiyar Daular Larabawa ta mika su don suyi zaman kaso.

Nicholas McGeehan, wanda kwararre ma'aikacin hukumar Human Rights Watch ne akan batutuwan ma'aikata 'yan cirani a yankin tekun Gulf, yace wannan 'babban batu ne', idan aka alakanta daya daga cikin manyan iyalai mafi arziki a duniya da fatauci da jama'a da kuma aikin bauta.

Yayi ikirarin cewa duk da hakan kaucewa doka ne, yin aikin bauta na ci gaba a kasashen yankin tekun Gulf."

Gimbiyoyin sun musanta tuhumar da ake musu, kuma BBC ta tuntubi lauyan da ke karesu don karin bayani.

An hana su abinci da ruwan sha.

An gabatar da karar a kotu ranar Alhamis, kuma da safiyar Jumma'a aka saurari lauyoyin dake kare wadanda ake tuhuma.

Batun ya fito fili ne a lokacin da daya daga cikin masu yin hidimar ta samu tserewa daga otel din da suka sauka.

Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da ita ta shaidawa gidan talabijin na Belgiyum cewa an tsare su a dakunan otel din kuma an sa masu gadi don hana su fita waje.

Bayan tuhumar da ake musu na zalunci, har ila yau ana zargin gimbiyoyin da laifukan rashin samar da takardun shiga kasar da suka dace da gazawa wajen biyansu albashi.

Ya ce," tabbas gimbiyoyin mutane ne masu martaba da daraja, su kuma wadanda abin ya rutsa da su mutane ne marasa galihu".

"Gimbiyoyin sun dauki kwararrun lauyoyi uku wadanda suka je babbar kotun Belgiyum domin kare su. Sai dai ba kowa ne yake da zarafin yin hakan ba".

Labarai masu alaka