Yaron da ya shekara 14 a kulle ya samu 'yanci

Isra'ila
Image caption Lamarin ya faru ne a garin Hadera a Isra'ila

'Yan sanda a Isra'ila sun kwato wani yaro mai shekara 14 da haihuwa, wanda iyayensa suka hana shi fita waje tun da aka haife shi, amma yanzu ana ba shi kula ta musamman.

Tashar Army Radio ta ce yaron ya fada wa 'yan sanda yadda iyayen nasa suke fita da shi harabar gidan nasu, da ke garin Hadera, sau daya ko sau biyu kawai a wata, yawanci ma a cikin dare.

Wasu lokuta kuma a kan ajiye shi a cikin wani keji da ke wajen gidan.

Iyayen yaron, wadanda tuni 'yan sanda suka kama su, sun ce sun dauki wannan matakin ne domin damuwar da suke da ita game da halin rashin lafiyar yaron.

Wasu makwabta ne suka kai kukansu zuwa ofishin karamar hukumar garin game da irin warin da yake fita daga gidan.

Wani mazaunin anguwar ya gaya wa tashar Army Radio cewa ya sanar da hukumomi batun ne bayan da ya ga yaron ta taga yana cikin wani hali "tamkar dodo a cikin wani fim".

"Naga idanunsa da yadda yanayinsa yake, lallai yana bukatar taimako ne. Sai na yanke hukuncin yin wani abu", in ji Chiko Waknin.

Iyayen yaron wadanda asalin su 'yan kasar Rasha ne ana ganin kamar sun kai 60 da haihuwa, kuma sun koma garin na Hadera da ke arewa da birnin Tel Aviv ne a shekarar 2009, amma basu sanar da hukumomi cewa suna da da ba, kuma ba su yi masa rajista a makaranta ba.

Wasu kafofin watsa labarai a garin sun ce lauyan uwar yaron ya fada musu cewa iyayen yaron sun so su "kare yaron ne saboda yana da matsalolin rashin lafiya".

Labarai masu alaka